An Tunowa Kabir Gombe Tsohon Wa’azinsa Yana 'Jinjinawa Tinubu' bayan Lashe Zabe

An Tunowa Kabir Gombe Tsohon Wa’azinsa Yana 'Jinjinawa Tinubu' bayan Lashe Zabe

  • Wani bidiyon maganganun Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe bayan zaben shugaban kasa yana yawo
  • Ana tunanin malamin ya yi maganar ne kwanaki bayan jam’iyyar APC ta doke PDP da sauran ‘yan adawa a zabe
  • Jama’a sun yi ca a kan malamin addinin musuluncin lura da halin da al’umma suka shiga a mulkin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - An lalubo wani tsohon bidiyon Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe yana magana bayan nasarar APC a zaben 2023.

A wannan bidiyo an ji malamin addinin musuluncin ya na kwararawa Bola Ahmed Tinubu yabo tun kafin ya shiga fadar Aso Villa.

Kabiru Gombe
Sheikh Kabiru Gombe ya yabi APC da aka yi nasara a zaben Najeriya Hoto: Muhammad Kabiru Haruna
Asali: Facebook

An tuno da maganar Kabir Gombe a Twitter

Wani ma’obocin dandalin X da ya fi shahara da Twitter ya wallafa bidiyon a ranar Laraba, ana magana kan kasuwar hannun jari.

Kara karanta wannan

Dada Yar’Adua zuwa Hakimin Bichi: Yadda aka rasa sarakai da fitattu 6 a awa 120

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir Kano yake cewa Allah SWT sa Kabiru Gombe ya ga wannan bidiyo domin ya iya ba da sabon alkaluma a halin da ake ciki.

Sheikh Kabir Gombe bayan cin zabe

Sheikh Kabiru Gombe yake cewa Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba za a gane ta, yana mai nuna za a ji dadi a mulkin Tinubu.

“Juma’a mai kyau tun daga Laraba muka gano. An rantsar da gwamnatin?
“Kasuwar hada-hadar hannun jari sun ba da sanarwa sun ce sun ci riba ta Naira Tiriliyan 1 daga lokacin da aka sanar da zabe zuwa yau.
“Suka ce daga shekara 50 zuwa yau ba a taba cin irin wannan ribar ba”

- Sheikh Kabir Gombe

Martanin da ake maidawa Kabiru Gombe

Mahadi Shehu ya rubuta:

“Daga inda malamai suka zama yan baranda, maroka, makwadaita, yan banbadanci, daga ranan a cika gaba da jiran tashin Alkiyama.

Kara karanta wannan

An soki Barau Jibrin kan karbar mutane zuwa APC alhali ana kukan kuncin rayuwa

"Yanzu kam duniya ta sa ma Kabiru Gwambe ido muji ko zai tabbatar da KWALIYA TA BIYA KUDIN SABULU”

Faysal King ya ce da yawan mutane sun daina daukar shehin a matsayin wani malami.

Abubakar Muhammad Bukar yana ganin kowa yana da kason laifinsa a halin da ake ciki.

“Kowa Da nasa kason. Duk abin da tinubu yayi. Harda ku aciki. Mai kyau ne mara kyau ne.

Abubakar Lawal Waziri kuwa ya dauki zafi, ya ce:

Munafukin Banza Allah Ya Isar Mana Akanku Malamai Maciya Amana Ƴan Son Duniya Yanzu Gashinan Yobe Ankashe Mutun 127 An Ƙara Kudin Mai Bakuce Komae Tunda Kunce Zanga Zanga Haramun Ce Malaman Izala Ƴan Siyasa Kunji Kunya Wallahi Kuma Allah Yana Kallon-Ku

Wani ya ce:

"Wannan fa ni ban daukesa malami ba, sune asalin masu ci da addini"
"Ina ruwan mu da wanni stock exchange Talaka kawai ya samu saukin rayuwa Kunlun policies marasa anfani Sai wahalar da talaka kawai ake haba..."

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya yi bakar addu’a ga masu mulki saboda karin kudin man fetur

- Inji MuF_deeny

Uncle Skuki yake cewa abin takaici ne a ce irin wadannan su ne jagororin kungiyar Izala, wasu kuma sun ba malamin kariya.

Wasu sun bayyana cewa a lokacin da Muhammadu Buhari ya yi nasara a kan PDP ne ya yi wannan magana ba a zaben 2023 ba.

Malamai na kuka da gwamnatin APC

Idan za a tuna, Bola Tinubu ya yi nasara a zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, ya doke Atiku Abubakar da Peter Obi.

Sai dai watanni da yin wannan magana sai ga shi malamai na kuka da gwamnati mai-ci, su ka nemi gwamnatin kasar ta gyara zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng