Dangote: NNPC Ya Ba Matatun Najeriya Ikon Sayar da Fetur Kai Tsaye ga 'Yan kasuwa

Dangote: NNPC Ya Ba Matatun Najeriya Ikon Sayar da Fetur Kai Tsaye ga 'Yan kasuwa

  • Gwamnatin tarayya ta ce matatun man Najeriya ciki har da ta matatar Dangote za su iya sayar da kayayyakinsu kai tsaye ga 'yan kasuwa
  • Ta bakin kamfanin man Najeriya (NNPCL), gwamnatin ta ce ko kusa ba ta adawa da matatar Dangotge, ko kayyade farashin fetur
  • Wannan dai martani ne da NNPCL ya yi ga wani ikirari na kungiyar kare hakkin Musulmi da ta ce kamfanin na yiwa Dangote zagon kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin mai na Najeriya (NNPC Ltd) ya bayyana cewa Dangote da sauran matatun man Najeriya na da ‘yancin sayar da fetur kai tsaye ga ‘yan kasuwa.

NNPC ya yi martani ne ga ikirarin da kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi a baya-bayan nan da ke nuna cewa kamfanin na adawa da matatar man Dangote (DRL).

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Dangote ba zai siyar da mai kasa da farashin kamfanin NNPCL ba'

Kamfanin NNPCL ya yi magana kan ikon Dangote na sayar da fetur kai tsaye ga 'yan kasuwa
NNPCL: "Dangote na da ikon sayar da fetur kai tsaye ga 'yan kasuwa." Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

MURIC ta zargi kamfanin NNPCL

Kamfanin man kasar ya bayyana matsayarsa ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC dai ta yi zargin cewa karin kudin fetur da NNPCL ya yi zai hana matatar Dangote sayar da fetur ga 'yan kasuwa a farashi mai rahusa.

Kungiyar kare hakkin Musulmin ta kuma zargi NNPCL da zama kamfani daya tilo da zai iya sayen kayan Dangote wanda hakan ke nuna tsantsar adawa da matatar.

Zargin MURIC: NNPCL ya wanke kansa

A martanin da ya mayar, kamfanin NNPCL ya fayyace cewa za a rika tsayar da farashin man fetur da suka hada da na matatar Dangote gwargwadon farashinsa a kasuwar man duniya.

Kamfanin NNPC ya kuma jaddada cewa tace mai a matatun cikin gida bai ba da tabbacin farashin fetur zai sauka idan aka kwatanta da farashinsa a duniya, batun da Dangote ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana kukan tsadar fetur, NNPCL ya fadi lokacin da mai zai wadata a kasa

"Matatar Dangote da sauran matatun man Najeriya na da 'yancin sayar da kayansu kai tsaye ga ’yan kasuwa a tsarin mai son saye da mai son sayarwa."

- A cewar NNPCL.

NNPCL ya kara kudin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya sanar da kara kudin man fetur zuwa N855 kan farashin lita da a baya ake siyarwa N568.

A yayin da matatar man Dangote ta sanar da cewa ta shirya fara sayar da feturin da ta tace, an ce wasu gidajen mai na musamman na NNPCL suna siyar da litar har N897 a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.