Sojoji Sun Hallaka Yan Ta'adda Sama da 150, Sun Ceto Mutum 91 da Aka Sace a Najeriya

Sojoji Sun Hallaka Yan Ta'adda Sama da 150, Sun Ceto Mutum 91 da Aka Sace a Najeriya

  • Hedkwatar tsaro watau DHQ ta bayyana nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan ƴan ta'adda a makon da ya gabata
  • Mai magana da yawun hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji sun kashe ƴan ta'adda 152, sun ceto mutane 91
  • Ya ce dakarun sun kwato makamai da dama kuma ba za su yi ƙasa a guiwa ba a ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ), a ranar Juma'a ta ce dakarun sojoji sun yi nasarar tura 'yan ta'adda 152 lahira tare da kama wasu 109 a makon jiya.

Bayan haka gwarazan sojojin sun ceto mutum 91 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa bama bamai a hedkwatar ƴan sanda, sun tafka ta'asa

Sojojin Najeriya.
Sojojin sun kawar da 'yan ta'adda 152, sun kama wasu 109 a mako guda Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka yayin da yake bayanin nasarorin sojoji a Abuja, Premium Times ta rahoto.

Sojoji sun ragargaji manyan ƴan bindiga

Buba ya ce a wannan mako da ya shige, sojojin sun kai samame kan wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda, Sadiku da Alhaji Yusuf, inda suka lalata maboyarsu.

Kakakin DHQ ya ce sojojin sun yi raga-raga da sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Sadiku da ke Tsaunin Tsora, ƙaramar hukumar Safana a Katsina.

Kazalika sojojin sun yi luguden wuta a sansanin ɗan bindiga Alhaji Yusuf wanda ke dajin Yadi a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, in ji Daily Trust.

Sojoji sun cafke mata masu alaƙa da ƴan ta'adda

Manjo Janar Buba ya ƙara da cewa sojoji sun cafke wasu mata biyu da ake zargin suna harkalla da ƴan bindiga wajen karɓo kuɗin fansar mutanen da suka sace.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya

Ya ce sojojin sun kuma kwato makamai kala daban-daban 183 da alburusai 4,443 daga hannun ƴan ta'adda a makon da ya shige.

Makaman da suka ƙwato sun haɗa da bindigogi kirar AK-47 guda 95, bindigogin gida guda 35, bindigun Dane 76, GPMG daya da kuma bindigogin PKT guda biyu.

Kaduna: An kashe babban ɗan bindiga

A wani rahoton kuma dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan da suka addabi mutane a Kaduna.

Sojojin sun hallaka wani shugaban ƴan ta'adda tare da mayaƙansa guda biyar yayin wani artabu a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262