‘Bari Tinubu Ya Dawo’ Sheikh Jingir Ya Dauki Zafi kan Karin Kudin Man Fetur
- Shahararren malamin Musulunci kuma shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a Jos ya yi magana kan karin kudin fetur
- Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce masu son bata gwamnatin Musulmi da Musulmi ne suka kara kudin man fetur
- Babban malamin ya ce yana da tabbas idan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya zai saurari koken talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a jihar Filato ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu kan tausayawa talakawa.
Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya yi magana ne kan karin kudin man fetur da aka yi a Najeriya.
Legit ta tatttaro abin da Sheikh Jingir ya fada ne a cikin wani bidiyo da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ana son bata sunan Tinubu' inji Jingir
Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya ce makiya tikitin Musulmi da Musulmi ne suka kara kudin man fetur.
Malamin ya ce sun kara kudin man fetur ne domin shafawa Bola Ahmed Tinubu kashin kaji a idon Musulmi masu son shi.
Ya ce saboda haka ne sai da suka bari shugaba Bola Tinubu ya tafi kasar Sin domin ayyuka na musamman, suka kara kudin fetur.
Jingir ya ce Tinubu zai saukakawa talaka
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce yana da tabbacin shugaban kasa Bola Tinubu zai ji koken talakawa idan ya dawo gida Najeriya.
Malamin ya ce ya fadi haka ne saboda Bola Ahmed Tinubu yana sauraron jama'a a lokacin da suka shiga damuwa.
Haka zalika malamin ya ce Bola Tinubu ya raba kudi ga gwamnoni da shinkafa ga ministoci domin su ba al'umma amma wasu sun ɓoye.
Kukah ya bukaci a rage kudin mai
A wani rahoton, kun ki cewa Rabaran Matthew Hassan Kukah ya yi kira ga gwamnatin tarayya a rage kudin man fetur da aka kara.
Faston ya ce a halin yanzu yan Najeriya na fama da yunwa saboda haka ya kamata a tausaya musu a rage kudin fetur a fadin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng