Tsadar Rayuwa: An Tausayawa Ma'aikata, Gwamna Ya Rage Kwanakin Zuwa Aiki

Tsadar Rayuwa: An Tausayawa Ma'aikata, Gwamna Ya Rage Kwanakin Zuwa Aiki

  • Gwamnatin jihar Ekiti ta dauki matakin rage kwanakin aiki ga kowane rukuni na ma'aikatan saboda tsadar fetur a Najeriya
  • A ranar Talatar makon da mu ke ciki ne kamfanin mai na NNPCL ya bayyana karin farashin litar fetur a fadin kasar nan
  • Lamarin ya jawo karuwar kudin ababen hawa da sauran kayan amfanin yau da gobe, abin da ya sa gwamnati daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ekiti - Gwamnatin Ekiti ta rage yawan kwanakin da ma'aikatanta ke zuwa aiki a mako saboda rage radadin karin farashin litar fetur.

Gwamna Biodun Oyebanji ne ya bayyana rage kwanakin, inda aka rage kwanakin da kananan ma'aikata za su rika fitowa a mako fiye da na manyansu.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Ekiti
Gwamnatin Ekiti ta rage kwanakin zuwa aiki Hoto: Government of Ekiti State, Nigeria
Asali: Facebook

A sakon da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook, gwamna Oyebanji ya cire wasu rukuni na ma'aikata daga cikin tsarin zuwa aikin da za a fara ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki nawa gwamnatin Ekiti ta ragewa ma'aikata?

Jaridar The Nation ta wallafa cewa gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya ce ma'aikata da ke mataki na daya zuwa bakwai za su rika zuwa aiki sau biyu a mako.

Wadanda ke mataki na takwas zuwa 12 za su rika zuwa aiki sau uku a mako, su kuma wadanda ke mataki na 13-17 za su rika zuwa aiki sau hudu a mako.

An ki rage kwanakin aikin wasu ma'aikata

Gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana cewa tsarin rage kwanakin aikin wasu ma'aikata zai dore na watanni biyu ne kacal, kuma ba duka ma'aikata ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kwamitin gwamnatin Kano zai fara binciken daidaikun mutane

Sanarwar da mashawarci na musamman ga gwamnan jihar, Yinka Oyebode ya fitar ta ce jami'an lafiya, malaman makaranta da jami'an tsaro ba sa cikin tsarin.

Gwamnati ta rage awannin aiki

A baya kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta dauki matakin saukakawa ma'aikata inda ta rage tsayin lokacin zuwa da tashi daga aiki albarkacin watan azumi.

A sanarwar da shugaban hukumar ma'aikatan jihar, Muhammad K Dagaceri ya sanyawa hannu, ya ce gwamnati ta rage awanni biyu daga lokacin zuwa aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.