'Abin da Ya Sa Bai Kamata Goodluck Jonathan Ya Sake Neman Takara a 2027 ba'

'Abin da Ya Sa Bai Kamata Goodluck Jonathan Ya Sake Neman Takara a 2027 ba'

  • Wata kungiyar mata da kananan yara ta shawarci tsohon shugaban kasa, Gooduck Jonathan kan neman takara a 2027
  • Kungiyar ta ce ya kamata Jonathan ya tsaya matsayinsa na dattijo ba tare da tsunduma a harkokin siyasa ba a yanzu
  • Shugaban kungiyar, Ogoegbunam Kingdom shi ya tabbatar da haka yayin da ya ke zantawa da jaridar Legit a wannan mako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Wata kungiya a Najeriya ta shawarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan tsayawa takara a 2027.

Kungiyar mai suna Platform for Youth and Women Development ta ce ya kamata Jonathan ya kauracewa neman takara a zaben.

An shawarci Jonathan kan sake tsayawa takara a zaben 2027
Kungiya ta gargadi Goodluck Jonathan kan sake tsayawa takara a 2027. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

2027: An ba Jonathan shawara kan takara

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Daraktan kungiyar, Ogoegbunam Kingdom shi ya bayyana haka yayin hira ta musamman da jaridar Legit.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kingdom ya ce ya kamata Jonathan ya janye kansa daga siyasa domin cigaba da kare mutuncin da ya ke da shi.

Ya bayyana irin gudunmawa da Jonathan ya ba dimukradiyyar Afirka da ma duniya baki daya.

Har ila yau, Kingdom ya caccaki masu kiran Jonathan ya nemi takara inda ya ce munafukai ne su suka yake shi a zaben 2015.

An bukaci Jonathan ya rike mutuncinsa

"Tun bayan barin ofis, Goodluck Jonathan ya ba da gudunmawa a cigaban dimukradiyya a Afirka da ma duniya baki daya."
"Ya kamata ya tsaya a matsayin dattijo ba tare da shiga cikin harkokin siyasa ba a wannan mataki da ya ke."
"Ya rike mukamai daban-daban daga mataimakin shugaban kasa zuwa mukaddashin shugaban kasa har zuwa shugaban kasa."

Kara karanta wannan

"Kun matsawa masu zanga zanga maimakon 'yan ta'adda," Atiku ya caccaki Tinubu

Ogoegbunam Kingdom

An fara maganan tsayawar Jonathan takara

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ƙasa ta nuna a shirye take ta marawa Goodluck Jonathan baya idan ya amince zai dawo a zaɓen 2027.

Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce dama ba a yi wa tsohon shugaban ƙasar adalci ba a sukar da aka masa kan tsaro.

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da aka fara kiraye-kirayen Jonathan ya sake fitowa takara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.