N1.3bn: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Martani kan Zargin Biyan Yan Ta'adda Kudin Sulhu

N1.3bn: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Martani kan Zargin Biyan Yan Ta'adda Kudin Sulhu

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta takardar da ke yawo ta na bayyana shirin biyan Biliyoyi ga 'yan ta'adda domin sulhu
  • Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubukar Nakwada ya ce gwamnatinsu na kan bakar ta na rashin sulhu da yan ta'adda
  • Ya ce takardar da aka rika cewa ta fito daga ofishinsa na shirin tattaunawa da yan ta'addan tsagwaron karya ce kuma ta bogi ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta da sanarwar da aka ce ta fito daga gare ta na shirin tattaunawa da yan ta'adda domin sulhu.

Kara karanta wannan

Bayan tura sojoji Sakkwato, 'yan Arewa sun fara shinshino karshen rashin tsaro

Sakataren gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Nakwada ne ya musanta takardar yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau.

Dauda
Gwamnatin Zamfara ta yi magana kan sulhu da yan ta'adda Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Radio Nigeria Kaduna ta wallafa Malam Nakwada na cewa takardar da ake cewa ta fito daga ofishinsa na fara shirin ganawa da jagororin yan ta'adda a jihar ta bogi ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta kafe kan kin tattaunawa da yan ta'adda

Jaridar Solace Base ta wallafa cewa gwamnatin Zamfara ta kafe kan matsayarta na kin tattaunawa da yan ta'adda da su ka addabi jihar

Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Nakwada ya ce a wannan matsayar suka fara mulki, kuma har yanzu su na kan wannan.

Zamfara: Gwamnati, yan sanda sun dauki mataki

Malam Nakwada ya ce gwamnatinsu ta yi takaicin labarin da ke cewa ta biya wasu masu yada labarai a kafafen sada zumunta domin fito da labarin sulhu da yan ta'adda.

Kara karanta wannan

"Kun matsawa masu zanga zanga maimakon 'yan ta'adda," Atiku ya caccaki Tinubu

Sakataren gwamnatin ya ce babu kamshin gaskiya a labarin, kuma yanzu haka yan sanda suna kan batun domin zakulo wadanda suka fitar da takardar bogin.

An zargi gwamnatin Zamfara da taimakon ta'addanci

A baya mun ruwaito cewa wata cibiya mai yaki da garkuwa da mutane ta CABT ta zargi gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare da hannu cikin ta'addanci a jihar.

A zargin da shugaban cibiyar, Yakubu Dauda ya yi, ya ce gwamna Dauda na biyan yan ta'adda suna hakar ma'adanai a jihar ba bisa ka'ida ba, inda ya nemi jami'an tsaro su dau mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.