Gwamnati Ta Fitar da Sharadin Sayarwa Ma'aikata Buhun Shinkafa kan N40,000
- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin fara sayar wa ma'akatanta buhun shinkafa mai girman kilo 50 kan N40,000
- Gwamnatin za ta fara sayarwa ma'aikata tan 30,000 na shinkafar kan farashi mai rangwame saboda tsadar rayuwa
- A cewar Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, sai ma'aikacin da ya ke da shaidar NIN za a sayarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dole sai ma'aikacin da ya mallaki katin shaidar dan kansa ta NIN da lambar waya za ta sayarwa shinkafa mai sauki.
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa gwamnati ta shirya sayarwa ma'aikatan tan 30,000 na shinkafa kan N40,000 kowane buhu mai nauyin kilo 50.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke kaddamar da fara sayarwa ma'aikata shinkafar a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsarin sayar wa ma'aikata shinkafa
Daily Nigerian ta wallafa cewa gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da cewa za ta sayarwa kowane ma'aikaci buhun shinkafa daya mai nauyin kilo 50 kan N40,000.
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa babu wanda gwamnati za ta ba shinkafa sama da buhu daya kan farashin mai sauki.
Gwamnati ta yabi tsarin sayar da shinkafa
Minista Abubakar Kyari ya bayyana tsarin sayar da shinkafar N40,000 ga ma'aikatan kasar nan a matsayin tallafi mai kyau daga gwamnati.
Ya ce shirin zai taimaka sosai, musamman idan aka yi duba da halin da talakawan kasar nan ke ciki da yunwa, tsadar abinci da rashin kudi.
Gwamna zai fara sayarwa ma'aikata shinkafa
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Ogun ta sayo tirelolin shinkafa domin sayarwa talakawa bisa farashi mai sauki domin rage masu radadin rayuwa.
Gwamna Dapo Abiodun ne ya yi wa ma'aikatan jihar albashir tare da alkawarin cewa gwamnati za ta sayar masu shinkafar a kan asalin farashinta kafin tashin Dala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng