Bayan Kara Kudin Mai: Gwamnati Ta Fadi Lokacin da Fetur Zai Wadata a Fadin Najeriya

Bayan Kara Kudin Mai: Gwamnati Ta Fadi Lokacin da Fetur Zai Wadata a Fadin Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa nan da karshen makon nan fetur zai wadata a fadin kasar, saboda haka jama'a su kwantar da hankula
  • Karamin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana hakan bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
  • Heineken Lokpobiri ya ce 'yan Najeriya su sani cewa gwamnati ba ta kayyade farashi ba, kuma wadatar fetur zai sa farashinsa ya daidaita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayar da tabbacin cewa za a samu wadatuwar man fetur a fadin kasar nan a karshen mako.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya Alhamis yayin da ya ke zantawa da manema labarai na Aso Rock bayan wata ganawa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarabawa sun yi adawa da karin kudin fetur, sun aika sako ga Tinubu

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan lokacin da fetur zai wadata
Ministan Tinubu ya roki jama'a su kwantar da hankali, fetur zai wadata.
Asali: Getty Images

NNPCL ya kara kudin fetur

Minista Lokpobiri ya ce an yi taron ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, wanda a cewarsa ya damu da irin wahalhalun da talakawa ke fuskanta, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata ne muka ruwaito cewa NNPCL ya aiwatar da karin farashin fetur daga N568-N617 zuwa N855-N897 a kan kowace lita (ya danganta da wurin da ake sayar da shi.)

Hakazalika ‘yan kasuwar mai sun daidaita farashinsu zuwa tsakanin N930 zuwa N1,250, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga 'yan kwadago da jama'ar kasar.

"Man fetur zai wadata" - Minista

Channels TV ta rahoto Lokpobiri ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji sayan fetur babu ji babu gani saboda tsoron za a iya samun karancinsa, yana mai cewa:

“Abin da ke da muhimmanci shi ne a rika samun fetur din a cikin kasar, kuma mun yi imanin cewa tsakanin yanzu zuwa karshen mako za a sami wadatar man a ko ina.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

“Amma abin da ke da muhimmanci shi ne gwamnati ba ta kayyade farashin. Muna kyautata zaton idan man ya wadata farashin ma zai daidaita."

Shettima ya kira taron gaggawa

Tun da fari, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya kira wani taron gaggawa na kusoshi a harkar fetur bayan karin kudin man.

Shettima ya saka labule da karamin ministan fetur, Heineken Lokpobiri, shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari da kuma mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.