Ku Shirya: Gwamnati Ta Bayyana Sunayen Jihohi 7 da Ambaliyar Ruwa Za Ta Yiwa Barna
- Gwamnatin tarayya ta ce akwai yiwuwar ambaliyar ruwa ta tafka barna a wasu jihohi bakwai a 'yan kwanaki masu zuwa
- Jihohin Benue, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Rivers da Bayelsa su ne wadanda ake hangen ambaliyar ruwan za ta fi yi wa barna
- Hukumar NEMA ta kuma shawarci jihohin da ke tsakiya da kudancin kasar nan su shirya tunkarar matsalar ambaliyar ruwan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi hasashen za a samu ruwan sama na kwanaki biyar wanda zai iya haifar da ambaliya a jihohi 21 da kuma wurare 123.
Gwamnati ta kuma shawarci wasu jihohin kasar da su shiryawa afkuwar ambaliyar ruwa da ka iya shafar garuruwansu musamman na kusa da rafuka.
Ambaliya a jihohin Najeriya 7
Haka kuma an lissafta jihohi bakwai wadanda da ta yi hasashen mamakon ruwan saman zai haifar da ambaliya da za ta yi masu illa sosai, inji rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin Benue, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Rivers da Bayelsa su ne wadanda ake hasashen ambaliyar za ta fi yi wa barna.
Hasashen ambaliyar ruwa da aka samu a ranar Alhamis daga ma’aikatar muhalli ta tarayya, ta kuma gargadi al’ummomin da ke kusa da kogin Benue da su yi taka-tsan-tsan.
Ambaliya: NEMA ta ba da matakan kariya
Jaridar This Day ta rahoto hukumar NEMA ta shawarci jihohin da ke tsakiya da kuma kudancin kasar da su shirya tunkarar matsalar ambaliyar ruwa.
Har ila yau, ta shawarci jihohi da su gyara magudanun ruwa da suka toshe, su gina shingen ambaliya na wucin gadi da kuma ficewa daga yankunan da ambaliyar ka iya shafa.
Hukumar ta NEMA ta bayar da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban sashin yada labaran ta, Manzo Ezekiel a ranar Alhamis.
Ambaliya ta yi barna a jihar Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi, ambaliyar ruwa ta afku a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.
An rahoto cewa sama da mutane 10,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da gonaki da wasu kadarorin miliyoyi suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng