Bayan Matawalle, an Zargi Gwamna Dauda da Hannu a ta'addanci, an Jero 'Hujjoji'

Bayan Matawalle, an Zargi Gwamna Dauda da Hannu a ta'addanci, an Jero 'Hujjoji'

  • Yayin da ake zargin Ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu a ta'addanci, an kuma saka sunan Gwamna Dauda Lawal
  • Cibiyar CABT mai yaki da garkuwa da mutane ta zargi Gwamnan da biyan yan ta'adda domin hakar ma'adinai ba ka'ida
  • Shugaban cibiyar, Yakubu Dauda shi ya yi wannan zargi inda ya bukaci jami'an tsaro su dauki tsattsauran mataki a kai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Wata kungiya ta zargi Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da daukar nauyin ta'addanci.

Cibiyar Centre Against Banditry and Terrorism (CABT) ta zargi gwamnan da hannu a cikin hakar ma'adinai ba na bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarabawa sun yi adawa da karin kudin fetur, sun aika sako ga Tinubu

An zargi Dauda Lawal na Zamfara da cin gajiyar ta'addanci a jihar
Kungiya ta zargi Gwamna Dauda Lawal da daukar nauyin ta'addanci. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

An zargi Gwamna Dauda da taimakawa ta'addanci

Babban daraktan cibiyar, Yakubu Dauda shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Legit ta samu a yau Alhamis 5 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan ya kuma ce ana zargin Dauda Lawal da biyan yan ta'adda da miyagu N1.3bn domin cigaba da samun riba a hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba.

Daga cikin wadanda ake zargin yana biyan akwai Kachalla Dogo Gide da Kachalla Bello Turji da Ado Alero da sauransu.

An bukaci jami'an tsaro su dauki mataki

Daga bisani, Dauda ya bukaci jami'an tsaro da su yi gaggawar daukar mataki kan wanda ake zargin, cewar rahoton Daily Post.

Ya kuma bukaci jami'an tsaron su kulle asusun bankunan da ake zargi tare da gurfanar da su a gaban shari'a.

"Wannan kudi da ake zargi an tura su ne a sirrance ta bangaren gwamnan wanda babu wani amincewa ko tabbatarwa daga Majalisar jihar kan haka."

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya tsira": Miyagu sun fasa ofishin gwamnan APC, sun yashe kaya

"Abin takaici har yanzu Gwamna Lawal bai yi karin haske kan zargin ba wanda shirunsa ke kara tabbatar da cewa shi abin zargi ne."

- Yakuba Dauda

Ta'addanci: Malamin Musulunci ya zargi Matawalle

Kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan shirin Bello Matawalle na yakar miyagun 'yan bindiga.

Shehin malamin ya caccaki gwamnati inda ya ce ba da gaske ta ke yi ba saboda yadda suka sanarwa duniya shirinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.