Ana Zaman Makokin Kisan Mutane 34, 'Yan Boko Haram Sun Sake Kai Hari a Yobe
- Rahotanni daga Buni Yadi, hedikwatar karamar hukumar Gujba a Yobe na nuni da cewa mayakan Boko Haram sun farmaki 'yan banga
- An rahoto cewa 'yan ta'addan sun dura sansanin 'yan bangar Buni Yadi a kafa inda suka bude wuta a wani yunkuri na kashe mutane
- Sai dai rundunar sojin Operation Lafiya Dole da kuma 'yan sandan jihar Yobe sun ce jami'an tsaro sun dakile harin duk da an yi barna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai sabon hari a jihar Yobe.
Harin da aka kai garin Buni Yadi, hedikwatar karamar hukumar Gujba a jihar Yobe, na zuwa ne ne kwanaki bayan mayakan ISWAP sun kashe sama da mutane 34 a Mafa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin na Buni Yadi ya afku ne a sansanin ‘yan banga da ke Sabon Fegi kusa da gidan gwamnati, a bayan sakatariyar karamar hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram ta kai hari a Yobe
Wata majiya daga garin ta shaida cewa ‘yan ta’addan sun kona wani sashe na gidan gwamnatin karamar hukumar da wasu motoci mallakar wani kamfanin burodi.
Majiyar ta ce:
‘’A daren jiya ne suka mamaye garin, inda suka kona wani bangare na gidan gwamnatin gwamnati tare da kona wasu motoci biyu mallakar wani kamfanin biredi.
"Yan banga da wasu jami’an tsaro ne suka yi artabu da ‘yan ta’addan, sun kona sansanin ‘yan banga, motoci biyu na kamfanin burodi da kuma wani sashe na masaukin."
Yobe: Jami'an tsaro sun magantu
Wata majiya daga hukumar tsaro ta ce daya daga cikin ‘yan banga da ke aiki a sansanin da aka kai harin ya samu raunuka.
An ce kafin harin, jami’an tsaro da ke sintiri sun kori jama’a daga kan tituna, bayan da suka samu labarin cewa 'yan ta'addan za su kawo harin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne a kafa.
Da aka tuntubi, Kyaftin Shehu Muhammad, mataimakin daraktan hulda da jama’a na sashen Operation Lafiya Dole da ke yankin Damaturu, ya ce sojoji sun yi nasarar dakile harin.
ISWAP ta dauki alhakin harin Yobe
A wani labarin, mun ruwaito cewa mayakan ISWAP sun fitar da wata wasika zuwa ga shugabanni da mazauna yankin Mafa suna masu daukar alhakin kashe mutane 34.
ISWAP ta ce ta kai hari yankin Mafa tare da kashe gomman mutanen ne domin zama martani ga cin amanar da mutanen yankin suka yi masu na hada kai da jami'an tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng