'Yan Bindiga Sun Sace Makusantan Malamin Musulunci a Arewa, Sun Kashe Direba

'Yan Bindiga Sun Sace Makusantan Malamin Musulunci a Arewa, Sun Kashe Direba

  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu 'yan uwan Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto har guda shida inda suke neman miliyoyin kudi
  • Malamin addinin wanda ya ce suna cikin tashin hankali ya roki Musulmi da su taimaka da abin da ya sawwaka domin hadawa a karbo su
  • A bayanin Sheikh Bashir Sani, ya ce 'yan bindigar sun kashe direban motar da makusantansa ke ciki suka ba karnuka namansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Bashir Ahmad Sani ya sanar da cewa 'yan bindiga sun sace wasu makusantansa shida.

Sheikh Bashir Sani ya ce 'yan bindigar sun yi garkuwa da makusantan nasa ne a kan wata hanya a Sokoto, kuma har sun kashe direban da ke jan motarsu.

Kara karanta wannan

Ana zaman makokin kisan mutane 34, 'yan Boko Haram sun sake kai hari a Yobe

'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a jihar Sokoto
Malamin addini ya nemi a yi masu karo karo domin karbo makusantansa da aka sace. Hoto: Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto
Asali: Facebook

An sace makusantan Sheikh Bashir Sokoto

A cikin wani faifan bidiyo da malamin ya fitar a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun mikawa karnuka naman direban da suka kashe sun cinye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Bashir Sani:

"Yan bindiga sun sace wasu makusanta na guda shida, kuma sun kashe direban motar sun jefawa karnai namansa sun cinye. Amma sauran suna ga hannun 'yan ta'addan.
"'Yan ta'addan sun ce sai an biya makudan kudi wajen karbo su. Miliyoyi masu matukar yawa suka nema, wadanda mutum ba ya tunani."

Malam na neman taimakon kudi

Malamin ya ce kowanene aka yiwa wannan ta'adi, akwai mahaifiyarsa, matarsa, 'ya'yansu guda biyu, kishiyar mahaifiyarsa da kuma kanwarsa.

Sheikh Bashir Sani ya ce:

"Don haka muke neman taimakonku 'yan uwa Musulmi domin mu dalibai ne almajirai wadanda ba mu da komai sai litattafai da muke karatu a kansu dare da rana.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kashe mutane 87 a Yobe, 'yan bindiga sun sake kai hari a jihar Arewa

"Muna neman taimako domin sun sanya lokaci na kai kudin, kuma sun ce idan ba a kai ba za su kashe su. Kuma dai kun ga abin da ya faru da Sarkin Gobir na Sabon Birni."

Malamin addinin ya kara jaddada bukatar taimakon jama'a na hada kudi domin karbo makusantan nasa, yayin da ya nemi addu'a daga 'yan kasar baki daya.

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan bindiga sun sace malami

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace wani malamin jami'ar tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara.

An rahoto cewa 'yan bindigar sun sace Bello Janbako, wanda babban malami ne a sashen nazarin addinin Musulunci na jami’ar a gidansa da ke Gusau, babban birnin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.