'Yan Bindiga Sun Sako Manoman Arewa a Gaba, Sun Gindaya Sharadin Girbe Gonaki

'Yan Bindiga Sun Sako Manoman Arewa a Gaba, Sun Gindaya Sharadin Girbe Gonaki

  • An gano yadda miyagu ke sha'aninsu a Arewacin kasar nan, yayin da su ka hana manoma shiga gonakinsu yin girbin damina
  • 'Yan bindiga sun sanya haraji mai nauyi kan manoma da ke son girbe amfanin gonakinsu a jihohin Zamfara, Neja da sauransu
  • Yanzu haka wasu daga cikin manoman sun bar yankunan, kuma sun yafe amfanin gonakin saboda harajin da aka nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Manoma a sassan Arewacin kasar nan sun shiga mugun hali bayan 'yan bindiga sun yanka masu haraji mai nauyi kafin su bari a girbe amfanin gona.

Jihohin da lamarin ya fi kamari sun hada da Zamfara, Neja, Katsina, Kaduna da Binuwai, inda duk manomin da ya bijirewa umarnin ke gamuwa da fushin miyagun.

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

Arewa
Miyagu sun sanyawa manoma harajin girbi Hoto: Dauda Lawal/Dr. Dikko Umaru Radda/Uba Sani
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta da Jaridar Nigerian Tribune, wasu daga cikin manoman da su ka kokarin girbe amfanin gonakinsu kan jawo miyagu su lalata gonarsa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manoma na barin gonakinsu a Arewa

Wani manomi a jihar Katsina da ya nemi a boye sunansa ya ce miyagun kan sanya haraji mai nauyi kafin girbi da kuma idan za su kai kaya kasuwa, wanda ya zarce kimar amfanin gonar.

Saboda haka da yawa daga cikinsu na barin gonakin, domin manomi mai kayan da bai kai Naira Miliyan biyu ba zai iya biyan harajin Naira Miliyan biyar ba.

Wasu Manoman Zamfara na biyan haraji

An gano wasu daga cikin manoman Zamfara kan biya haraji lokaci zuwa lokaci ga miyagu domin su samu damar nomawa da girbe amfanin gonakinsu.

Wuraren da aka gano hakan sun hada da Maru, Maradun, Zurmi, Gusau, Bakura, Anka, sai kuma Moriki da Magarya a karamar hukumar Zurmi.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

'Yan bindiga sun sanyawa manoma haraji

A wani labarin kun ji cewa 'yan bindiga na neman hana noma a yankin jihar Zamfara bayan sun dora harajin Naira Miliyan 200 kan manoman da ke Zurmi.

Miyagun sun sanya harajin a kan kauyuka 10, inda tuni wasu su ka fara biya, sauran kuma na kokarin nemo kudin domin su tsira da rayukansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.