An Gano Yadda Ake Shigo da Makamai Najeriya, Gwamnati Ta Dauki Mataki
- Gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a tashar ruwa ta Onne biyo bayan yawan shigo da makamai ba bisa ka'ida ba ta jihar Ribas
- Shugaban hukumar kwastam Bashir Adeniyi ne ya tabbatar da hakan, ya ce za a tsaurara matakan sanya ido kan kayan da ake shigowa da su
- Shugaban ya kara da cewa shigo da makaman da ake yi ta yankin kalubale ne babba ga tsaron kasar nan da lafiyar al'ummar da ke Onne
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a kan tashar ruwa ta Onne da ke jihar Ribas biyo bayan shigowa da makamai da ake yi ta yankin.
Shugaban hukumar kwastam na kasa, Bashir Adeniyi ne ya bayyana haka, inda ya ce shigo da makamai da ake yi ta yankin babbar barazana ce ga zaman lafiya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Bashir Adeniyi ya shaidawa manema labarai cewa daga yanzu, gwamnati za ta sanya tsatstsauran mataki a kan kayan da ke biyowa ta yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati za ta fara duba makamai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara sanya idanu kan kwantena da ke shigowa ta tsahar ruwan Onne a Ribas domin kama makaman da ake shigowa da su.
Shugaban hukumar kwastam na kasa ne ya bayyana haka, inda ya ce matakin zai taimaka wajen dakile ayyukan miyagu a cikin kasar nan, Independent Newspaper ta wallafa.
Gwamnati ta fadi illar shigo da makamai
Shugaban kwastam na kasa, Bashir Adeniyi ya ce gwamnati ta na sane da illar shigo da makamai cikin kasar nan.
Babban jami'in ya shaidawa manema labarai cewa shigo da makaman babbar barazana ce ga mazauna Onne da zaman lafiyar Najeriya ba ki daya.
An zargi gwamnati da sanin matsalar tsaro
A baya kun ji cewa babban malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya zargi gwamnatin tarayya da masaniya a kan matsalar tsaro.
Shehin malamin ya caccaki gwamnati, inda ya ce babu abin da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle bai sani ba a kan matsalar tsaro a yankinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng