Gwamnatin Buhari Ta Fadi Hakikanin Abin da Ya Faru kan Cire Tallafin Man Fetur

Gwamnatin Buhari Ta Fadi Hakikanin Abin da Ya Faru kan Cire Tallafin Man Fetur

  • Mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi bayani kan tallafin mai
  • Bashir Ahmad ya bayyana dalilin da ya sa Buhari ya ki saka kudin tallafin mai a dukkan kasafin kudin shekarar 2023
  • Haka zalika, Bashir ya fadi yadda Bankin Duniya da IMF suka rika saka Buhari a gaba kan cire tallafin mai da karya Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi magana kan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Jami'in tsohon shugaban kasa a harkar yada labarai, Bashir Ahmad ne ya fadi dalilin saka kudin tallafi na watanni shida a 2023.

Kara karanta wannan

"Ya yi ta'aziyya": Bashir Ahmad ya fadi dalilin rashin zuwan Buhari jana'izar Dada

Bashir Ahmad
Dalilin fara rage kudin tallafin mai da Buhari ya yi a 2023. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da Bashir Ahmad ya yi ne a cikin wani bidiyo da RFI Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IMF ta matsawa Buhari ya cire tallafin mai

Bashir Ahmad ya bayyana cewa Bankin Duniya da IMF sun matsawa Buhari lamba kan cire tallafin man fetur a shekaru takwas da ya yi.

Sai dai ya ce ko sau daya Muhammadu Buhari bai taba niyyar cire tallafin man fetur ba saboda illar da zai haifar a Najeriya.

Dalilin kin saka kudin tallafin mai a 2023

Bashir Ahmad ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya saka tallafin mai ne a kasafin kudin shekarar 2023 na watanni shida kawai.

A cewar Bashir, Buhari ya yi haka ne domin kar ya yi katsalandan ga shugaban da zai zo daga baya a kan harkar tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

"A yi amfani da tsarin IBB": Janar Akilu ya ba Tinubu shawarar magance rashin tsaro

Bashir ya ce dukkan gwamnatin da ta biyo baya tana da damar saka kudin tallafin kuma saboda haka Buhari ya fita daga zargi.

IMF ya bukaci a karya darajar Naira

Bashir Ahmad ya bayyana cewa Bankin Duniya da IMF sun bukaci Muhammadu Buhari ya karya darajar Naira.

Sai dai ya bayyana cewa Buhari bai taba aiki da maganar ba sai sau daya a 2017 kuma daga nan ya ga abin ba zai yi kyau ba, ya watsar da zancen.

An yi zanga zangar tsadar mai a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Delta a Kudancin Najeriya sun nuna cewa wasu matasa sun yi zanga zangar karin kudin mai.

An ruwaito cewa matasan sun toshe hanyoyi wanda hakan ya kawo tsaiko kan harkokin kasuwanci a yankin da abin ya faru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng