'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Gida, Sun Sace Jigon PDP bayan Yi wa Iyalinsa Barazana
- Wasu yan bindiga da ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kutsa a gidan jigon jami'yyar PDP a jihar Oyo
- Miyagun sun shiga gidan Cif Benedict Akika inda su ka rika yiwa jama'ar gidan barazanar harbe su idan su ka ce uffan
- Tun kafin su shiga gidan 'dan siyasar, miyagun suka rika harbin iska domin firgita jama'ar kusa da gidan kamar yadda aka ji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo - Wasu miyagu da ake kyautata zaton masu garkuwa da jama'a ne sun sace jigo a jam'iyyar PDP a jihar Oyo, Cif Benedict Akika har gidansa.
Miyagun sun rika harbin iska a lokacin da su ka shiga unguwar Cif Akika da ke Olorunda a karamar hukumar Lagelu a jihar Oyo.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa bayan miyagun sun yi nasarar kutsawa gidan ne su ka kara jan kunnen mutanen ciki da kar su ce uffan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sace jigon jami'yyar PDP
Jaridar Punch ta wallafa cewa yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai farmaki gidan jigon jami'yyar PDP da ke Oyo, Cif Benedict Akika a daren Laraba.
Daya daga cikin makusantan Cif Akika da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa dan siyasar na zaune ya na hutawa da iyalansa a lokacin da miyagun su ka far masu.
Martanin yan sanda kan sace jigon PDP
Wasu mazauna unguwar Olarunda sun bayyana cewa an sace Cif Akika kwanaki kadan bayan ya kammala rabon tallafi ga mata a karamar hukumar Lagelu.
Zuwa lokacin hada wannan labari, rundunar yan sandan jihar ko kakakinta, Adewale Osifeso ba su ce komai kan garkuwar ba.
Yan bindiga sun harbe 'dan PDP
A wani labarin kun ji cewa wasu miyagu sun harbe jigo a jam'iyyar PDP da ke jihar Enugu, Ejike Ugwueze a hanyarsa ta garin Neke Odenigbo.
Da ya ke tabbatar da afkuwar kisan jigon, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Enugu, DSP Daniel Ndukwe ya ce miyagun sun zagaye shi kafin su harbe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng