Jihohi 4 Sun Shiga Matsala, Tinubu Ya ba Su Wa'adin Kwanaki 5 kan Kafa 'Yan Sandan Jiha
- Yayin da aka shirye-shiryen kirkirar yan sandan jihohi, an ba jihohi hudu wa'adin kwanaki biyar domin kawo rahotonsu kan lamarin
- Jihohin da ake zance sun hada da Adamawa da Kebbi da Sokoto da kuma jihar Kwara sannan da birnin Tarayyar Najeriya watau Abuja
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin gwamnan Oyo, Bayo Lawal ya fitar a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kwamitin tattalin arziki (NEC) ya yi zama a birnin Tarayya Abuja kan lamuran da suka shafi ƙasar a Aso Rock.
Yayin taron kwamitin, an ba jihohin Najeriya hudu wa'adin kwanaki biyar kan kawo rahoto game da kafa yan sandan jihohi.
Yan sandan jiha: Tinubu ya ba jihohi wa'adi
An gudanar da taron ne a Abuja wanda mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya jagoranta, cewar rahoton TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da aka ba wa'adin sun hada da Kwara da Adamawa da Kebbi da Sokoto da kuma birnin Abuja, Daily Post ta ruwaito.
Kwamitin ya bukaci jihohin su tabbatar sun kawo rahotonsu zuwa 9 ga watan Satumbar 2024 kan ƙirƙirar yan sandan jihohi.
Za a dauki mataki kan jihohin 4
Mukaddashin gwamnan jihar Oyo, Bayo Lawal shi ya tabbatar da haka bayan kammala taron NEC a yau Laraba.
Lawal ya ce kwamitin zai dauki tsattsauran mataki kan jihohin idan ba su kawo rahoton zuwa 9 ga watan Satumbar 2024 ba.
"A yau ne duka jihohin ake tsammanin su mika rahoto kan kirkirar yan sandan jiha saboda kwamitin ya yi dub a kai, amma an samu jihohi hudu da ba su cika ka'idar ban"
- Bayo Lawal
Egbetokun ya ki amincewa da yan sandan jihohi
Kun ji cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana matsayar rundunar ‘yan sandan Najeriya kan shirin kirkiro da ‘yan sandan jihohi.
A wani taron tattaunawa na yini daya kan lamarin a Abuja a Afrilun 2024, IGP Egbetokun ya ce Najeriya ba ta shirya amfani da ‘yan sandan jihohi ba.
Sufetan 'yan sandan ya bayyana cewa kirkirar ‘yan sandan jihohi zai haifar da rikicin kabilanci, wanda zai kai ga rashin jituwa a jihohin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng