Hakimin Bichi, 'Dan Autan Marigayi Sarkin Kano Bayero Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Hakimin Bichi, 'Dan Autan Marigayi Sarkin Kano Bayero Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Masarautar Kano ta shiga alhini bayan sanar da rasuwar Hakimin Bichi, Alhaji Idris Abdullahi Bayero a jihar
  • An sanar da rasuwar marigayin wanda shi ne Barden Kano kafin rasuwarsa a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izarsa a fadar Sarkin Kano da misalin karfe 1.00 da rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar Hakimin Bichi, Alhaji Idris Abdullahi Bayero.

Marigayin wanda kafin rasuwarsa shi ne Barden Kano ya rasu a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.

Hakimin Bichi ya riga mu gidan gaskiya a Kano
An yi sallar jana'izar marigayi Hakimin Bichi, Alhaji Idris Abdullahi Bayero. Hoto: @SanusiSnippets.
Asali: Twitter

Kano: Hakimin Bichi ya kwanta dama

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban kasa ya shiga taron NEC da manyan attajirai 2, bayanai sun fito

An bayyana rasuwar marigayin a shafin @SanusiSnippets na X a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin shi ne dan autan marigayi Sarkin Kano, Abdullahi Ado Bayero wanda kafin rasuwarsa ya mulki kasar shekaru 27.

Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa da misalin karfe 1.00 na rana a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Sarki Sanusi II ya jagoranci sallar jana'iza

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar jana'izar a fadarsa da ke jihar da ranar yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.

Sallar jana'izar ta samu halartar manyan mutane daga masarautar da kuma manyan jami'an gwamnati da sauran al'umma.

Idris Abdullahi Bayero shi ne ɗan autan marigayi Sarkin Kano, Abdullahi Bayero, wanda ya yi mulki daga 1926 zuwa 1953.

An fara naɗa Alhaji Idris Bayero a 1990 a matsayin Ɗan Darman Kano kuma hakimin Rimin Gado ta hannun ɗan uwansa, marigayi Sarki Ado Bayero, wanda ya yi sarauta daga 1963 zuwa 2014.

Kara karanta wannan

"Ya yi ta'aziyya": Bashir Ahmad ya fadi dalilin rashin zuwan Buhari jana'izar Dada

Aminu Ado ya kaddamar da gyaran fadarsa

Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya kaddamar da fara sabunta masarautar Nassarawa da ke jihar.

Wannan mataki na tsohon Sarkin ya dauki hankulan jama'a yayin da ake cigaba da rigimar masarautun jihar.

Wasu na ganin wannan wani mataki da yake nuna himmatuwar tsohon Sarkin na cigaba da kasancewa a kujerar sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.