An Ƙara Zuga Tinubu Ya Lafta Haraji a Najeriya, Bill Gates Ya ce Kudin Ya yi Kadan
- Shahararren mai kudi a duniya, Bill Gates ya kawo ziyarar aiki tarayyar Najeriya domin tattaunawa kan muhimman abubuwa
- Bill Gates ya bayyanawa cewa kudin haraji da ake karba a Najeriya ya yi kadan kuma hakan ba zai kawo cigaba a kasa ba
- Maganganun Bill Gates sun zo daidai da lokacin da gwamnatin Bola Tinubu take kokarin kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10%
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban mai kudi a duniya, Bill Gates ya yi magana kan yadda ake karɓar haraji wajen yan Najeriya.
Bill Gates ya nuna cewa dole idan ana son ayyukan cigaba a Najeriya a kara kuɗin harajin da ake karba a kasar.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Bill Gates ya yi magana ne bayan gwamnatin tarayya ta fara shirin kara haraji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kara harajin VAT a Najeriya?
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da shirin kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10% ga al'ummar kasar.
Legit ta ruwaito cewa a halin yanzu gwamnatin tarayya ta mika bukata ga majalisar dattawa domin tabbatar da dokar karin harajin.
Billa Gates: 'Haraji ya yi kadan a Najeriya'
Shahararren mai kudin duniya, Bill Gates ya ce harajin da gwamnatin tarayya ke karba a wajen yan kasa ya yi kadan.
Bill Gates ya zo Najeriya ne domin tattaunawa kan muhimman abubuwa da suka shafi ilimi da kiwon lafiya.
Amfanin kara haraji a Najeriya
Daily Trust ta wallafa cewa Bill Gates ya bayyana cewa kara harajin zai saka abubuwa su daidaita a Najeriya kamar yadda aka dade ana buƙatar hakan.
Ya ce harkar ilimi da kiwon lafiya za su bunkasa ne idan gwamnatin tarayya tana samun kudin haraji yadda ya kamata.
Shettima ya fadi amfanin karbar haraji
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce akwai alheri mai yawa kan tsarin karban haraji da gwamnati ta kawo.
Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin da zai yi kwaskwarima kan kasafin kudi da karbar haraji a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng