Gobara Ta Lakume Sashen Babban Asibiti a Arewa, Gwamna Zai Dauki Mataki

Gobara Ta Lakume Sashen Babban Asibiti a Arewa, Gwamna Zai Dauki Mataki

  • Wata mummunar gobara ta jawo asarar kayan duba marasa lafiya na makudan kudi a babban asibitin jihar Adamawa
  • A ziyarar duba irin asarar da aka yi, Gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri ya zargi makiya ci gaba da haddasa gobarar
  • Ya dauki alkawarin gyara ba tare da bata lokaci ba, inda ya bukaci jama'a da su taimakawa gwamnati wajen tsare asibitin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - Wata gobara da ta tashi a asibitin kwararru mallakin gwamnatin Adamawa da ke Jimeta- Yola ta kone sashen adana bayanai da kayan aiki.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin shekaru uku da asibitin ke fadawa cikin iftila'in gobara tare da jawo asarar kayan aiki na miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya dauki mataki da gobara ta tashi a gidan gwamnati

Gobara
Gobara ta lalata sashen asibitin Adamawa Hoto: Pius Iliya
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, babban mai taimakawa gwamnan Adamawa kan yada labarai, Pius Iliya, gwamna Ahmadu Fintiri ya zargi marasa son ci gaba da haddasa gobarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara: Gwamnatin Adamawa za ta gyara asibiti

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za bata lokaci wajen gyara babban asibitin jihar da gobara ta lalata ba.

AIT ta wallafa cewa wutar ta tashi a daren Talata, wanda hakan ya jawo tsaiko kafin jami'an kashe gobara su samu damar kai daukin da zai kashe wutar.

Ana duba marasa lafiya a asibiti duk da gobara?

Kwamishinan lafiya a jihar Adamawa, Felix Tangwami ya bayyana cewa gobarar da ta tashi a babban asibitin jiha ba zai kawo matsala wajen duba marasa lafiya ba.

Ya bayyana cewa sashen da gobarar ta tashi, wuri ne da ake ajiye wasu kayan aiki da bayanai, saboda haka za a ci gaba da duba lafiyar jama'a.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina, ta shafi bangaren ofishin gwamna

Gobara ta tashi a Adamawa

A baya kun ji cewa gobarar da ta tashi a wata kasuwa da ke Adamawa, ta yi sanadiyyar lalata shaguna da dukiyoyi masu tarin yawa da ba a tantance adadinsu ba.

A jawabinta kan gobarar, mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta ta ce duk da ba san yawan asarar ba, gwamnati za ta iya rage asarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.