Mai Tsoron Mutuwa Shi ne Gawar Fari," Sojojin Najeriya Sun Ja Kunnen Bello Turji
- Wasu zaratan sojojin kasar nan sun gargadi kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji kwanaki kadan bayan ya wallafa wani bidiyo
- An hango Bello Turji da yaransa a bidiyon suna kona motocin sulken sojojin kasar nan da aka bari bayan sun makale a cikin tabo
- A bidiyon matasan sojojin, sun zarge shi da cewa shi matsoraci ne mai kashe mutanen da ba za su iya daukar wani mataki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Bidiyon wasu matasan sojoji guda uku ya dauki hankalin jama'a bayan an jiyo su suna gargadin kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji.
Fusatattun matasan sojojin sun roki Bello Turji da rabu da sace jama'a da kashe mutanen da ba za su iya rama cin zalin da ya ke yi masu ba, ya fuskance su.
A wani bidiyo da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, sojojin sun zargi Bello Turji da cewa shi matsoraci ne mai kashe mutanen gari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon sojojin na zuwa kwanaki kadan bayan Bello Turji da yaransa sun rika yada bidiyo a shafukan sada zumunta inda su ka kona motocin sojoji guda biyu makale a tabo.
Sojoji sun ja kunnen Bello Turji
Sojojin kasar nan sun gargadi Bello Turji da cewa ya na dab da gamuwa da mutuwarsa, domin a cewarsu;
"Makashin maza, maza kan kashe shi."
Sojoji na takaicin harin Bello Turji
A bidiyon da wani mai amfani da shafin Facebook, Abubakar Abdullahi ya wallafa, an ji sojojin su na sanar da Bello Turji cewa sun shirya idan shi ma ya shirya.
Matasan sun bayyana takaicin yadda Bello Turji ya makale daga wani wuri ya na kai farmaki kan yan Najeriya da ba su yi masa komai ba.
Sojoji za su kakkabe miyagu
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin kasar nan sun fara daura damarar yakar yan ta'addan da da su ka hana Arewa maso Yammacin kasar nan zaman lafiya.
Wannan ya zo bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba sojojin umarnin su koma Sakkwato, tare da yakar ta'addanci da yan ta'addan har sai an samu sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng