Gwamnonin Arewa Sun Yi Martani Mai Zafi kan Harin 'Yan Ta'adda a Yobe

Gwamnonin Arewa Sun Yi Martani Mai Zafi kan Harin 'Yan Ta'adda a Yobe

  • Ƙungiyar gwamnonin Arewa ƙarƙashin jagorancin Inuwa Yahaya, ta yi Allah wadai kan harin da ƴan ta'adda suka kai a jihar Yobe
  • Gwamnonin yankin sun buƙaci jami'an tsaro da su tabbatar cewa an zaƙulo miyagun da suka kai harin domin su fuskanci hukunci
  • Ta yi ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu ga gwamnatin Yobe kan mummunan ta'addancin da ƴan ta'addan suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Gombe - Shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da harin da ƴan ta'adda suka kai a jihar Yobe.

Gwamna Inuwa ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka yi asarar rayuka da dama a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe sakamakon harin na ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukuma, sun hallaka jami'an tsaro

Gwamna Inuwa ya magantu kan harin Yobe
Gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai kan harin da 'yan ta'adda suka kai a Yobe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa Gwamna Inuwa kan harkokin yaɗa labarai, Ismaila Uba Misilli ya sanya a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnonin suka ce kan harin?

Gwamnan ya yi kakkausar suka kan wannan ɗanyen aikin, yana mai bayyana shi a matsayin aikin rashin hankali wanda ya jefa mutane cikin halin jimami.

Inuwa ya yabawa jami’an tsaro kan ci gaba da ƙoƙarin da suke yi na yaƙar ragowar ƴan ta’adda, inda ya jaddada buƙatar su ƙara ƙaimi wajen zaƙulo miyagun da suka yi wannan ta’addancin.

"Bai kamata a ƙi yin hukunci kan wannan ɗanyen aikin ba. Ina kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙoƙarin da suke yi tare da tabbatar da cewa an gaggauta hukunta waɗanda suka aikata laifin."

- Gwamna Inuwa Yahaya

Gwamna Inuwa ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma gwamnatin jihar Yobe, inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙansu tare da yiwa waɗanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun shiga uku": Gwamna ya sha alwashi kan matsalar tsaro

Tinubu ya yi Allah wadai da harin Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta bayyana takaici kan harin ƴan kungiyar ISWAP da ya salwantar da rayukan mazauna Mafa, a ƙaramar Tarmuwa a jihar Yobe.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da an hukunta miyagun 'yan kungiyar ISWAP da suka kashe mutane 87 a Yobe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng