"A Yi Amfani da Tsarin IBB": Janar Akilu Ya ba Tinubu Shawarar Magance Rashin Tsaro
- An ba gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawarar yadda za ta iya magance matsalar tsaron da ke ci gaba da ta'azzara a kasar
- Tsohon shugaban hukumar leken asiri, Birgediya-Janar Halliru Akilu (mai ritaya), ya ce gwamnati ta waiwayin tsarin ECOMOG
- Janar Akilu ya ce ECOMOG ya ba gwamnatin tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida nasara a yaki da rashin tsaro
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ghana - Tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya, Birgediya-Janar Halliru Akilu (mai ritaya), ya ba gwamnatin Shugaba Bola Tinubu shawara kan dawo da tsaro.
Birgediya Janar Akilu ya bukaci shugabannin Najeriya da su yi koyi da tsarin da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya dauka na magance matsalar rashin tsaro.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke jawabi a taron VIC kan nasarorin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida a Ghana, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Ali Akilu ya tuna mulkin IBB
Janar Akilu ya ce a mulkin Babangida na shekaru takwas, Najeriya ta sha fadawa cikin wuyacin hali, amma a kullum ya na daukar kwararan matakai na dawo da zaman lafiya.
Ya ce shugabanci ne da aka tsara ba wai don tafiyar da al’amuran Nijeriya kawai ba, har ma da jagorantar yankin yammacin Afirka da Afirka baki daya.
"Gwamnati ta yi imani da aza harsashin wanzar da zaman lafiya, inganta hadin gwiwar yanki da kuma sauye-sauyen tattalin arziki a fadin nahiyar."
"A kwaikwayi tsarin IBB" - Ali Akilu
Janar Akilu ya shawarci shugaban kasar da ya kara yin nazari sosai kan sauye-sauyen da IBB ya yi a fannin tsaro, inji rahoton PRNigeria.
A cikin sauye sauyen akwai raba rusasshiyar hukumar tsaron Najeriya (NSO) zuwa sababbin hukumomin tsaro guda uku: DIA, NIA da kuma DSS.
Ya jaddada cewa:
“A yanzu ne lokacin da ya kamata shugabanni su yi koyi da tsarin ECOMOG da gwamnatin Babangida ta yi amfani da shi na magance rashin tsaro da tattalin arziki."
Shinkafi ya magantu kan ta'addanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, shugaban kungiyar PAPSD ya bayyana matsalar cin hanci da rashawa, fatara da jahilci a matsayin tushen rashin tsaro.
Dakta Shinkafi ya nemi gwamnonin Arewa da su daina wahalar da kansu ko kashe kudi wajen shirya taruka a kasashen waje da sunan neman hanyar magance matsalar tsaron yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng