Gwamnonin PDP Sun Fusata da Kalaman Wike, Sun Hada Shi da Jami'an Tsaro

Gwamnonin PDP Sun Fusata da Kalaman Wike, Sun Hada Shi da Jami'an Tsaro

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi martani kan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya yi
  • Ƙungiyar gwamnonin a wata sanarwa ta bayyana kalaman tsohon gwamnan Rivers a matsayin waɗanda ba su dace ba
  • Ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro su ankara da barazanar da ya yi ta kunno wuta a jihohin da ke ƙarƙashin ikon PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar PDP sun mayar da martani kan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi.

A wani jawabi dai da Wike ya yi, ya gargaɗi gwamnonin PDP masu tsoma baki cikin rikicin siyasar jihar Rivers kan cewa zai kunno musu wuta a jihohinsu.

Kara karanta wannan

An fadi dalilin da ya kamata ya sanya PDP ta hukunta ministan Tinubu

Gwamnonin PDP sun caccaki Wike
Gwamnonin PDP sun yiwa Wike martani Hoto: @OfficialPDPNig, @govwike
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Emmanuel Agbo, darakta-janar na ƙungiyar gwamnonin PDP, ya nemi hukumomin tsaro da su ankara da furucin na Wike, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani gwamnonin PDP suka yi?

Gwamnonin sun bayyana kalaman Wike a matsayin waɗanda ba su dace ba kuma ba za a yarda da su ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Barazanar da Wike ya yi na kunno wuta a jihohin PDP ba ta dace ba domin koma baya ne ga ƙoƙarin kawo haɗin kai da mutunta juna tsakanin shugabanni da 'yan jam'iyyar."
"Abin takaici ne hakan ya fito daga bakin wani wanda mamba ne a wannan ƙungiyar mai daraja a matsayinsa na tsohon gwamna."
"Ƙungiyar tana kira ga hukumomin tsaro na ƙasa da su ankara da kalaman Wike na kunno wuta a jihohin domin babu wanda yafi ƙarfin doka."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi lokacin kawo karshen rikicin jam'iyyar

- Emmanuel Agbo

An ba jam'iyyar PDP shawara kan Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar North East Unity Forum (NUF) ta buƙaci PDP ta hukunta ministan babban birnin tarayya Abuja.

Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin jam’iyyar PDP da su hukunta Nyesom Wike domin dawo da ɗa’a a cikin jam’iyyar mai adawa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng