Gwamnonin Arewa Sun Haɗa Kai, Sun Fitar da Matsaya kan Wargaza Yan Bindiga
- Gwamnonin Arewacin Najeriya sun dauki matakin hada kai domin kawar da yan bindiga da suka addabi yankin da kashe kashe
- Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka yayin da ya karbi rahoto kan tsaron jihohin yankin
- Gamayyar kungiyoyin Arewa karkashin kungiyar CNG ce ta fitar da rahoto kan hanyar magance matsalar yan bindiga a Arewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe ya bayyana matakin hadin kai da gwamnonin Arewa za su dauka domin maganin yan bindiga a yankin.
Shugaban gwamnonin Arewa, gwamna Inuwa Yahaya ya ce matsalar tsaro na kawo tsadar kayayyaki a Najeriya baki daya.
Daraktan yada labaran gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ne ya wallafa jawabin gwamnan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan tsaro
Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce za su hada kai domin tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki kan matsalar yan bindiga.
Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnonin Arewa za su shirya wani babban taro da zai tatttaro masana domin ganin an wargaza yan bindiga a Arewa.
Rashin tsaro a Arewa da tsadar abinci
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnoni sun damu kan yadda matsalar yan bindiga ke hana noma a Arewacin Najeriya.
Shugaban gwamnonin ya ce matsalar rashin tsaro ce ta haifar da tsadar abinci da tashin farashin kayayyaki a Najeriya.
Arewa: An mika rahoton tsaro ga Tinubu
Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa, Bashir Yusuf Ibrahim ya ce sun mika rahoto kan yadda za a magance yan bindiga a Arewa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bashir Yusuf Ibrahim ya bayyana cewa rahoton ya kunshi dogon nazari da aka yi a Arewa domin samar da cikakken tsaro.
Gwamnoni sun fitar da tsari kan tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Arewa maso Yamma sun ce sun samar da tsarin magance matsalar tsaro a shiyyarsu.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ne ya bayyana hakan a karshen taron kwana biyu kan tsaro da shirin UNDP ya shirya a Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng