Jerin Jihohin Arewa da Aka Fi Yawan Sace Mutane cikin Shekara 1 a Najeriya
Jihohin Arewa musamman a bangaren Yammaci suna fama da matsalolin ta'addanci da kuma garkuwa da mutane da ya yi katutu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara su ne kan gaba wurin fama da matsalar wadanda dukansu ke Arewa maso Yamma.
An sace mutane fiye da 7, 500 a Arewa
Rahoton SM Violence Tracker da Legit ta samu ya tabbatar da cewa an sace mutane 7,568 cikin shekara 1 a kasar a lokuta 1,130 daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta ruwaito cewa akalla N1bn ne aka biya na kudin fansa ga 'yan ta'adda a cikin shekara daga watan Yulin 2023 zuwa Yunin 2024.
Legit Hausa ta tsakuro muku wasu daga jihohi na Arewacin Najeriya da abin ya fi shafa.
1. Jihar Zamfara
Jihar Zamfara ce kan gaba inda aka yi garkuwa da mutane akalla har sau 132 wanda ya yi sanadin sace mutane 1,639.
2. Jihar Kaduna
Kaduna ta zamo ta biyu inda aka sace jama'a sau 113 wanda yawan mutane da aka sacen ya kai 1,113.
3. Jihar Katsina
Jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma ita ce ta uku inda aka sace mutane 887 a lokuta akalla 119.
4.Jihar Borno
A Borno da ke Arewa maso Gabas wacce ke fama matsalar Boko Haram, an sace mutane 720 a lokuta daban-daban har 63.
5. Jihar Niger
Niger da ke yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya ita ta kasance ta biyar inda aka sace mutane sau 48 da ya yi sanadin garkuwa da mutane 689.
6. Jihar Sokoto
Sokoto ta kansace ta shida wacce ke Arewa maso Yamma inda aka sace mutane 487 a lokuta har sau 67.
Sauraren wuraren da ake sace mutanen Arewa
Sauran sun hada da birnin Tarayya Abuja da aka sace mutane 404 sai Benue da mutane 186 sai kuma Kogi da aka sace mutane 170.
Har ila yau, akwai jihar Taraba da mutane 167 sai Bauchi da mutane 114 da kuma Nassarawa da mutane 113.
Garuruwan Arewa masu saukin garkuwa da mutane
Jihohin Arewa da ba a samu matsala sosai ba su ne Gombe inda aka sace mutane biyu a lokaci daya sai Kano da aka sace mutane biyu a lokuta sau hudu.
Sai kuma jihar Jigawa da mutane 2 a lokuta biyu da Yobe mai mutane tara a lokuta takwas sai kuma Adamawa mai mutane 11 a lokuta har sau 13.
Akwai Plateau da aka sace mutane 26 a lokuta 24 da Kebbi mai mutane 26 a lokuta 10 sai kuma ta karshe Kwara mai mutane 80 a lokuta daban-daban har sau 27.
Tattaunawar Legit Hausa da hadimin Gwamna Inuwa
Legit Hausa ta tattauna da hadimin Gwamna Inuwa Yahaya kan wannan nasara da jihar Gombe ta ke samu.
Hadimin gwamnan a bangaren sadarwa ta zamani, Yusuf Alyusra ya ce tabbas Gwamna Inuwa yana bakin kokari wurin dakile matsalolin tsaro.
"Gaskiya ka san daman jihar Gombe Allah ya albarkace mu da zaman lafiya kuma shugabanninmu da malaman addinin da jami'an tsaro suna iya kokarin wajen ganin mun cigaba da wannan zaman lafiya."
"Ko a mako da ya gabata Mai girma Gwamna, Alh. Muhammad Inuwa Yahaya ya gayyaci dukkan wadanda alhakin kula da tsaro ya rataya a kansu suka tattauna kan abubuwan da ya shafi tsaro."
- Yusuf Alyusra
Alyusra ya ce ko shakka babu irin wadannan matakai suna ba da gudunmawa sosai wajen cigaban zaman lafiya da ake samu da kuma addu'oi da al'umma suke yi.
Bello Turji ya kona motocin sojoji
Kun ji cewa an yada wani faifan bidiyo mai tayar da hankali da 'yan ta'adda ke bankawa motocin sulke na sojoji wuta.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng