'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku: Gwamnati Ta ba Hafsoshin Tsaro Umarnin Tarewa a Sokoto
- Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya umurci babban hafsan tsaro na kasa da sauran hafsoshin tsaro da su koma jihar Sokoto
- An ce ministan ya dauki wannan matakin ne da nufin ƙara tsananta ayyukan soji a jihar domin kawar da barazanar da ‘yan bindiga ke yi
- Umarnin ya jaddada kudirin gwamnati na maido da zaman lafiya da tsaro a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, da Kebbi da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya umurci babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, tare da wasu hafsoshin tsaro da su koma jihar Sokoto.
Da wannan umarnin, shugabannin sojojin za su kula da hare-haren sojoji kan 'yan ta'addan daga Sokoto, da nufin dakilewa da kuma kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Yamma.
Za a tsaurara yaki da ta'addanci
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an ba da umarnin ne a matsayin martani ga ayyukan 'yan bindiga da kuma yadda lamarin tsaro ya ke ci gaba da tabarbarewa a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan umarnin ya kuma biyo bayan hare-haren 'yan bindiga da suka yi kamari a jihar Sokoto, ciki har da kisan wani basarake a kwanan baya.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, jihar Sokoto, wadda ita ce hedikwatar rundunar soji ta 8 za ta kasance sansanin da za a gudanar da gagarumin atisayen kawar da 'yan ta'adda a shiyyar.
An ce Bello Matawalle zai kasance a cikin tawagar shugabannin sojojin da za su kula da ayyukan sojojin na kakkabe 'yan ta'adda musamman Bello Turji da tawagarsa.
Minista ya tura hafsoshi Sokoto
Wata sanarwa daga ofishin karamin ministan na cewa:
“Karamin ministan tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana bakin cikinsa kan ayyukan ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi da kewaye.
“Saboda haka ne ministan ya umurci babban hafsan tsaron kasa da sauran hafsoshin soji da su koma Sokoto wadda ita ce hedikwatar GOC Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi.
"Yayin da suke yankin Arewa maso Yamma, za su sa ido kan yadda sojoji za su gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da an kakkabe Bello Turji da ’yan tawagarsa.”
Bello Turji ya kona motocin soji
A wani labarin, mun ruwaito cewa rikakken dan bindigar nan da ya addabi Sokoto, Bello Turji ya fitar da wani bidiyo da ya ke nuna ya kwace wasu manyan motocin yakin sojojin Najeriya.
A cikin bidiyon, an ga yadda yaran Bello Turji suka kwace dukkanin makamai da alburusan da ke cikin motocin biyu, daga bisani kuma suka cinna masu wuta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng