DHQ Ta Yi Martani kan Batun Kwace Motocin Sojoji da 'Yan Bindiga Suka Yi a Zamfara

DHQ Ta Yi Martani kan Batun Kwace Motocin Sojoji da 'Yan Bindiga Suka Yi a Zamfara

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta fito ta yi magana kan bidiyoyin da ƴan bindiga suka yaɗa inda suka yi iƙirarin ƙwace motocin soji
  • Daraktan yaɗa labarai na DHQ, ya bayyana cewa motocin maƙalewa suka yi a cikin taɓo ba ƙwace su ƴan bindigan suka yi ba
  • Manjo Janar Edward Buba ya kuma musanta cewa ƴan bindiga sun sace mutum 150 yayin wani hari a jihar Sokoto

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta musanta cewa cewa ƴan bindiga sun ƙwace motoci masu sulke guda biyu na sojoji a jihar Zamfara.

DHQ ta kuma musanta iƙirarin cewa an hallaka mutane masu yawa waɗanda ƴan ta'adda suka binne tare da rahotannin sace mutum 150 a Sokoto.

Kara karanta wannan

Sabuwar zanga zanga ta ɓarke a Abuja, matasa sun aika sako ga Shugaba Tinubu

DHQ ta musanta kwace motocin sojoji a Zamfara
DHQ ta ce 'yan bindiga ba su kwace motocin sojoji ba a Zamfara Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun yi iƙirarin ƙwace motoci

Martanin na DHQ na zuwa ne bayan wasu bidiyoyi sun yaɗu wanda suke nuna ƴan bindiga na murnar ƙwace motocin sojojin, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana bidiyoyin a matsayin na ƙarya, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da zancen.

Meya faru da motocin sojoji a Zamfara?

Da yake bayani kan abin da ya faru a Zamfara, Edward Buba ya bayyana cewa motocin sun maƙale ne a cikin taɓo yayin da suke ƙoƙarin farmakar ƴan bindigan a ƙauyen Kwashabawa.

Ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun cire kayayykin da ke da amfani a cikin motocin domin hana ƴan bindigan yin amfani da su.

Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa bidiyon da aka yaɗa wanda ya nuna ƴan ta'adda na binne mutane masu yawa ba a ƙasar nan ya faru ba.

Kara karanta wannan

Tofa: Ƴan sanda sun bayyana Bature da ya nemi kifar da gwamnatin Tinubu a Najeriya

DHQ ta musanta sace mutum 150 a Sokoto

Ya bayyana cewa jita-jitar da aka yaɗa kan cewa an sace mutane 150 a Sokoto, an yaɗa ta ne domin a dusashe nasarar da sojoji suke samu kan ƴan ta'adda.

Sojoji sun hallaka shugaban ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya (NAF) sun samu nasarar hallaka wani shugaban ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Sojojin sun hallaka shugaban ƴan ta'addan ne mai suna Mustapha Abdullahi tare da wasu mayaƙa guda biyar a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng