N70000: Gwamnan APC Ya Bayyana Lokacin da Zai Fara Biyan Ma'aikata sabon Albashi

N70000: Gwamnan APC Ya Bayyana Lokacin da Zai Fara Biyan Ma'aikata sabon Albashi

  • Gwamna Francis Nwifuru ya sanya farin ciki a fuskokin ma'aikatan jiharsa ta Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • A ranar Asabar din nan ne Gwamna Nwifuru ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan gwamnatin Ebonyi
  • Gwamna Nwifuru ya bayyana hakan ne a lokacin bikin doya na Ojiji Izhi, inda kuma ya soki yadda ake tafiyar da kwangilolin Jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi, ya amince da biyan N70,000 matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnatin jihar.

Gwamna Nwifuru ya bayyana hakan ne a lokacin bude babban bikin doya na Ojiji Izhi, a ranar Asabar, 31 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dauko kammala aikin Kwankwaso, ya yiwa dan kwangila barazana

Gwamna Francis Nwifuru ya yi magana kan fara biyan sabon mafi karancin albashi a Ebonyi
Ebonyi: Gwamna Francis Nwifuru zai fara biyan ma'aikata sabon albashin N70000. Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Twitter

Ebonyi: Ma'aikata za su samu N7000

Jaridar The Punch ta ruwaito Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na umarci hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su tsara hanyoyin biyan sabon mafi karancin albashin da zai fara aiki daga watan Satumba.
"Na san cewa akwai bambanci kan mafi karancin albashi da kuma karawa ma'aikata albashi. Sabuwar dokar mafi karancin albashi ta N70,000 ta shafi kowa.
"Mafi karancin albashin ba wai karin albashi ba ne; ka da ma'aikata su dauka za a kara N70000 kan albashinsu na yanzu ne, hakan ba zai yiwu ba."

'Yan kwangila sun fusata gwamna

Sai dai gwamnan ya fusata kan yadda wasu manyan shugabannin jihar ke gudanar da kwangilolin da gwamnatin jihar ta ba su.

Gwamnan ya nuna bacin ransa kan lamarin, musamman wadanda aka ba kwangilar gidajen da ke unguwar Izo da ke a karamar hukumar Ishielu.

Kara karanta wannan

"Muna kan aiki," Gwamna ya faɗi matakin da ya ɗauka kan biyan sabon albashin N70,000

Ya kwamishinan gidaje umarni na ya tabbatar da an kammala fentin gidajen a cikin karamin lokaci.

Gwamna Nwifuru ya kuma yi kira ga mazauna jihar da kada su yi kasa a gwiwa wajen kai rahoton jinkirin ayyukan gwamnati da ‘yan kwangila ke yi.

Adamawa: Sabon albashi ya fara aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Adamawa ta fara biyan ma'aikatanta sabon mafi karancin albashi na N70,000 a karshen watan Agusta.

Hakan ya biyo bayan alkawarin da gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ya dauka a ranar 19 ga watan Agustan na fara biyan sabon albashin a karshen watan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.