"Akwai Jan Aiki a Gaba": Yadda 'Yan Najeriya Za Su Magance Matsalolin kasar da Kansu
- An yabawa shugaba Bola Tinubu kan jawabin da ya yiwa ‘yan kasa kan zanga zangar da aka kammala kwanan nan a fadin kasar
- Titilope Anifowoshe, wata mai sharhi kan lamuran jama'a, ta bukaci Shugaba Tinubu da ya aiwatar da alkawuran da ya dauka a jawabinsa
- Titilope Anifowoshe ta bayyana cewa matsalar Najeriya ba ta shugabanci ba ce, matsala ce ta dabi'un jama’a a kan abin da ya shafi gina kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar mai sharhi kan al'amuran jama'a, Titilope Anifowoshe, ta yi nazari kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya tafiyar da zanga-zangar yunwa da aka kammala kwanan nan.
A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng, lauyar ta ci gaba da cewa zanga-zangar da aka kammala ta na cike da sarkakiya, kuma za a iya kallonta a mahanga da dama.
Zanga-zanga: Nazari kan jawabin Tinubu
Ta kara da cewa kalaman Tinubu na dauke da bayanai masu jan hankali amma kuma ya jefa mutane cikin shakku kan abin da gwamnati ke yi na magance yunwa a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Titilope Anifowoshe ta bayyana cewa:
"Zan iya cewa ba a taba sauraron jawabin kai tsaye da shugaban ya yi ba, domin ya nuna zurfin fahimtarsa kan matsalolin da suka addabi al'ummarmu.
"Sai dai kuma, jawabin nasa ya jawo tsoro da rashin tabbas a zukatan jama'a, domin ya yi magana ne kan cuta ba tare da samar da magani ba, kowa ya san halin da ake ciki.
"Tambayar da kowa ya ke yi a yanzu ita ce: shin za mu iya magance wadannan matsalolin a kan lokaci, ko kuwa lokaci ya riga da ya kure mana?"
Dabarun magance matsalolin Najeriya
Ta ci gaba da cewa, matsalar Najeriya ba ta shugabanni kadai ba ce, har da ta ta al’ummar kasar. Ta kuma ce za a iya yiwa Tinubu alkalanci ne kawai da aikinsa ba da jawabinsa ba.
Ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa:
"Matsalar Najeriya ba ta shugabanni kadai ba ce. Mu ma 'yan kasar akwai rawar da za mu iya takawa. Dole mu yi aiki tukuru, mu hade kanmu tare da sanya kasarmu gaba da komai.
"Dole ne tun daga kan ma'aikatan gwamnati, ciyamomi, 'yan majalisun jiha da na tarayya, sarakuna da gwamoni, da duk wani shugaba su hada kai domin ci gaban kasarmu."
Lauyar ta ce akwai jan aiki a gaban Tinubu, tana mai cewa kalaman shugaban kasar na da tasiri amma rashin aiwatar da su ya jawo koma baya ga kasar.
Matashin dan siyasa ya magantu
A zantawarmu da Abbas Aliyu Tanko, wani matashin dan siyasa daga Funtua, jihar Katsina, ya bayyana cewa har sai 'yan kasa, musamman matasa sun tashi tsaye lamura za su daidaita.
Mai neman takarar shugaban karamar hukumar ta Funtua, ya ce shugabanni kadai ba za su iya magance matsalar kasar ba, wannan wani aiki ne da ke bukatar gudunmawar kowa.
Abba Tanko ya nuna cewa Najeriya ta kowane bangare na da ma'adanai da albarkatun kasa da idan aka sarrafa su za su iya magance matsalolin kasar da dama.
Matashin ya ce manyan matsalolin kasar ba sa rasa nasaba da rashin ayyuka da tsadar rayuwa wadanda farfado da masana'antu da samar da ayyuka za su iya magancewa.
Tinubu ya yi jawabi kai tsaye
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin kai tsaye ga al'umar Najeriya a ranar Laraba, 12 ga watan Yunin 2024.
Wannan jawabin ya alamta zagayowar ranar dimokuraɗiyyar Najeriya, kuma Shugaba Tinubu ya dauki alkawura da dama da za su iya kawo babban sauyi ga lamuran kasar.
Asali: Legit.ng