Mata Sun Zargi Rundunar Sojojin Kasa, Sun Nemi a Janye Dakaru daga Yankin Ibo

Mata Sun Zargi Rundunar Sojojin Kasa, Sun Nemi a Janye Dakaru daga Yankin Ibo

  • Mata inyamurai sun zargi sojojin kasar nan da jawo masu matsaloli fiye da dakile ayyukan bata gari a yankinsu
  • Wasu daga cikin matan karkashin kungiyar National Igbo Women ta zargi sojojin da neman na goro a hannun masu bin hanyoyi
  • Kungiyar IWA ta nemi rundunar sojoji ta janye wadanda aka turo yankunansu saboda rashin amfanin kasancewarsu a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Kungiyar mata Inyamurai ta nemi gwamnatin tarayya da ta janye dakarunta da aka girke a sassa daban-daban da ke Kudu maso Gabashin kasar nan.

Matan sun zargi sojojin da takurawa mabiya hanyoyin yankin su ta hanyar karbar na goro yayin da miyagu ke cin karensu ba babbaka a kusa da shingensu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu kai wa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi a Arewa maso Gabas

Sojoji
Mata Ibo sun nemi a janye dakarun sojoji daga yankinsu Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugabar matan, Lolo Nneka da ta yi kiran a Enugu ta ce abin kunya ne yadda sojojin ke ajiye aikinsu su na neman cin hanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa ana kallon yadda miyagu ke dauke mutane a kusa da shingen sojojin, amma ba sa iya hana su migun aikin.

Mata Ibo sun nemi a kori sojoji

Kungiyar IWA ta nemi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kori sojojin da ke yankunansu na kabilar Ibo domin a cewarsu, ba su da amfani.

Shugaban kungiyar, Lolo Nneka ta shawarci gwamnati ta karfafawa yan sanda domin ba su damar kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin Kudu maso Gabas.

Mata sun koka kan kiyayyar Ibo

Kungiyar mata inyamurai ta koka kan yadda Yarbawan kasar nan ke kin jininsu, musamman a jihar Legas da ke kan gaba wajen nuna kiyayya gare su.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Lolo Nneka ta bayyyana mamakin abin da ya sa ake kin jininsu ba tare da gwamnati ta yi yunkurin daukar matakin dakile hakan ba.

Ibo sun ki shiga zanga zanga

A baya mun ruwaito cewa matasan kabilar Ibo sun bi sahun sauran 'yan Najeriya wajen gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da aka gudanar.

Kungiyar Ohaneaze Ndibo ce ta bayyana haka da ta ke zantawa da manema da labarai, inda ta ce ba za su yi zanga-zanga ba bayan tattauna matsalolin da yankin ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.