'Mun San Komai': Ma’aikaci Ya Fallasa Barnar da Aka Rika Yi a Mulkin Ganduje a Kano

'Mun San Komai': Ma’aikaci Ya Fallasa Barnar da Aka Rika Yi a Mulkin Ganduje a Kano

  • Aminu Lawal Hassan ya zargi gwamnatin da ta shude a jihar Kano da karkatar da kudin gyaran makarantu
  • Jami’in ya yi ikirarin kungiyoyin kasashen waje sun saba turowa makarantu kudi da nufin inganta harkar ilmi
  • A maimakon a yi abin da ya kamata, ana zargin ana yin gaba da kudin, akasin abin da yake faruwa a yau

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Aminu Lawal Hassan ma’aikaci ne a jihar Kano wanda a ‘yan kwanakin nan yake fallasa wasu abubwaun da ke faruwa.

Aminu Lawal Hassan ya yi magana bayan jin tsohon kwamishinan ilmi ya na martani kan gyaran makarantu da ake yi a Kano.

Gwamnatin Kano
Ana zargin ana ba daidai ba a Gwamnatin Kano Hoto: @KYusufAbba/@Dawisu
Asali: Twitter

Kano: Jami'in SBMB ya fasa kwai

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

A matsayinsa na jami’in SBMB ya yi karin haske a shafin Facebook a kan irin kudin da aka rika aikowa makarantun gwamnatin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi Kiru wanda ya yi kwamishinan ilmi a gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje ya ce ba da kudin gwamnati mai-ci ake yin ayyukan ba.

Yadda aka rika turowa makarantun Kano kudi

Hassan yake cewa lokacin APC ta na mulki kungiyoyin kasashen duniya su kan turowa makarantu kudi kai-tsaye domin a inganta su.

Maimakon ayi amfani da kudin wajen gyaran banɗaki, sayen kujeru da kofofi ko tagogi, ya ce ana karkatar da su zuwa wani asusun.

A labarin da ya ba da, ya bayyana cewa ya san abin da ya rika faruwa, ya ce matsayarsa sai da ta jawowa makarantarsa matsala.

Saboda ya ki maida kudin da aka aiko ne a karshe gwamnatin baya ta tsame makarantar daga cin moriyar duk wasu tsare-tsare.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Kano ta yi magana kan shirinta, akwai gyare gyare

Gwamnan Kano ya sa ido a asibitin Bayero

Bayan fallasa abubuwan da suka faru a makarantu a lokacin sai kuma aka ji shi ya yi rubutu a Facebook kan barnar da ake yi a asibiti.

Ma’aikacin ya jawo hankalin gwamnatin Abba Kabir Yusuf cewa ta saka ido a kan abubuwan da ke faruwa a asibitin Hasiya Bayero.

Ya ce saboda ana raba maganguna kyauta a asibitin, ta kai cewa marasa lafiya su na zuwa tun daga kauyuka har zuwa wajen jihar Kano.

Wannan dafifi da ake yi ya ba wasu ma’aikata damar karbar kudi a hannun masu jinya domin su hada su da likitan da zai duba su.

A karshe ya roki gwamnati ta rage kudin gwaji kuma a gyara sauran asibitocin da ke karkara.

“Saboda gyara da samar da kayan aiki da magani kyauta da ake Bayarwa a asibitin yasa mutane suke dafifi, zuwa asibitin, bincike ya nuna banda marasa lafiya daga ƙauyukan Kano harda makotan Jihohi.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

"Wannan ya sa kasuwar yan chuwa chuwa ta bude kafin ka ga likita, ko karban magani sai ka san wani ko kuma an san HANNUN KA, Mai yiwuwa shugabanin asibitin ba su san da wannan chuwa chuwar da kananan ma'aikatan su ke yi ba.”

- Aminu Lawal Hassan

Dan Bello ya jikawa gwamnan Kano aiki

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana a kan zargin badakalar magunguna kamar yadda rahoto ya zo kwanakin baya.

Abba ya umarci a fara binciken zargin da ake yi na cewa an cire kudi daga kananan hukumomi, aka turawa kamfanin Novomed.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng