Ganduje ya ware N880m domin gyara makarantun Gwamnati a Jihar Kano
Mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware fiye da Naira miliyan 800 da nufin gyara makarantun boko na gwamnati da ke jihar.
Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai kashe wadannan makudan kudi ne domin ganin an dawo da darajar makarantun gwamnati a jihar.
Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje za ta batar da Naira miliyan 20 a kowace karamar hukuma, adadin jimillar abin da za a kashe shi ne Miliyan 880.
Za a zabi makaranta guda ne a kowace karamar hukuma kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana. An fitar da wannan rahoto ne a ranar Lahadi.
Kwamishinan ilmi na jihar Kano, Sanusi Kiru ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da ‘yan Najeriya bayan an kaddamar da wannan shiri a jiya.
Kiru ya kuma shaida cewa gwamnatin Kano ta na shirin bude sababbun makarantun mata 130 a fadin jihar, wadanda za su taimakawa ilmin ‘ya ‘ya mata.
KU KARANTA: Mun batar da N3.4b a kan harkar ilmi a Kano - Gwamna
A cewar kwamishinan za a bude wadannan makarantu ne a kananan hukumomi 24. Za a kafa manyan makarantu 75, da makarantun sakandare 55.
“Gwamnatin jiha da hadin-kan babban bankin Duniya za ta gyara wasu makarantun gwamnati domin bunkasa karatun ‘ya ‘ya mata.” Inji Sanusi Kiru.
Mai girma kwamishinan ya kara da cewa: “Gwamnatin jihar Kano ta kuma ware Naira miliyan 880 da za a gyara makaranta guda a kowace karamar hukuma.”
Kwamishinan ya ce an kafa wani kwamiti na manya da za su yi kokarin ganin an yi wannan aiki. An kaddamar da shirin ne a ranar 30 ga watan Agusta, 2020.
Kiru ya ce za a biyawa yaran da su ka fadi WAEC kudin jarrabawar NECO da NBAIS. Sannan ba a samu wanda ya kamu da COVID-19 cikin masu jarrabawa ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng