Kano: Abba Ya Ja Kunnen Jami’ai, An Karyata Zancen Saida Filin Masallacin Idi

Kano: Abba Ya Ja Kunnen Jami’ai, An Karyata Zancen Saida Filin Masallacin Idi

  • Mai girma Abba Kabir Yusuf ya waiwayi wadanda ake zargin suna yanka filayen gwamnatin Kano ba bisa ka’ida ba
  • Gwamnan ya ja kunnen masu wannan aika-aika tare da kiran jama’a su tona masu asiri, ya ce doka za ta yi a kansu
  • Kafin nan hukumar KNUPDA mai kula da tsarin birnin jihar Kano ta karyata zancen sake yanka filin masallacin idi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta musanya zargin cewa ana saida wasu filaye a masallacin Idi da ke Kofar mata a jihar Kano.

Shugaban hukumar KNUPDA ya bayyana haka da rade-radi suka fara yawo cewa an dawo yankawa ‘yan kasuwa wuri a masallaci.

Kara karanta wannan

'Mun san komai': Ma’aikaci ya fallasa barnar da aka rika yi a mulkin Ganduje a Kano

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano ya ja kunnen masu yanka filayen gwamnati Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

An sake yanka filin masallacin idin Kano?

A wani taron manema labarai da ya kira wanda tashar Nasara ta dauko labarin, Arch. Ibrahim Yakubu Adamu ya yi wani karin haske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na KNUPDA mai alhakin tsara birane ya bayyana cewa babu gaskiya a zancen raba wurin ibadan al’ummar da aka karbe.

Ibrahim Yakubu Adamu ya ce babu fili a masallacin Kofar Mata da aka saida ko aka raba sai dai yunkurin gina wurin taron addini.

Menene abin da ya faru da filin masallacin idi?

Hukumar ta ce filin da ake surutu a kai bai cikin masallaci, wani dadadden wuri ne da ke kallon Kofar Wambai da ake yin kasuwanci.

KNUPDA ta ce akwai masu teburori da suka dauki fiye da shekaru 20 suna neman na abinci a wannan wuri a wajen masallacin idin.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Gwamnan Kano ya ja-kunnen jama'a

Ana haka sai aka ji sanarwa cewa gwamnan Kano ya nemi al’umma su sanar da hukuma da zarar sun ji ana cefanar da filin gwamnati.

A wata sanarwa da aka gani a shafin Salisu Yahaya a Facebook, an ji Mai girma Abba Kabir ya ce ya ji labarin ana taba filayen jihar Kano.

“Duk wani asibiti, makaranta, makabarta, masallaci ko wajen shakatawar al'umma mallakin gwamnati da kuka ga ana kokarin yankawa a siyar ku sanar mana domin a dauki matakin gaggawa.
“Mai girma gwamna yace nan gaba ba iyaka masu yankawa su siyar za'a dinga hukuntawa ba, har mutanen da suke saka kudadensu suna siyan irin wayannan gurare hukunci zai bi ta kansu.”

- Gwamnatin Kano

Gargadi kan masu taba filin gwamnatin Kano

Sanarwar da aka fitar a shafin tashar Freedom ta ce Alhaji Abduljabbar Garko ya ja kunnen mutane kan taba filayen gwamnatin jiha.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Garko shi ne Kwamishinan kasa da tsare-tsare kuma shugaban kwamitin kula da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kano.

Abba ya dage da ayyuka a jihar Kano

Bayan korafin jama’a, ana da labari cewa an ga ‘yan kwangila sun dukufa sun koma aikin tituna a wasu unguwannin dake jihar Kano.

Alamu sun nuna Abba Gida Gida da gaske yake yi wajen farfado da martabar ilmin zamani a jihar, ana ta gyara kanana makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng