Kisan Gilla: 'Yan Sanda Sun Tono Gawar 'Yan banga, An Kama Basarake

Kisan Gilla: 'Yan Sanda Sun Tono Gawar 'Yan banga, An Kama Basarake

  • Rundunar yan sandan Akwa Ibom ta tono gawar wasu yan banga da miyagu suka yiwa kisan gilla suka birne su a wani kabari
  • Kakakin yan sanda a jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John ya tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi
  • Haka zalika Timfon John ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai basaraken Utit Antai mai suna Okon Asuquo Etoekpo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom - Rundunar yan sanda ta tabbatar da cafke wasu mutane da ake zargi da kisan yan banga.

Haka zalika rundunar ta tono yan bangar a kabarin da aka birne su domin yin cikakken bincike kan kisan gillar da aka musu.

Kara karanta wannan

Yara 'yan kasa da shekara 18 sun tafi kurkuku kan 'yunkurin' kifar da gwamnati

Akwa Ibom
An tono kabarin yan banga a Akwa Ibom. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cikin wadanda yan sanda suka kama akwai basaraken yankin Utit Antai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tono gawar yan banga

Rundunar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tono wasu yan banga da aka yi wa kisan gilla aka birne su yayin binciken wadanda ake zargi da kisan.

Kakakin yan sandan jihar Akwa Ibom, Timfon John ya ce sun samu kan gawarwakin ya fara wargajewa.

Wadanda ake zargi da kashe yan banga

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa bayan samun labarin kisan ta tsananta bincike domin kama miyagun da suka aikata laifin.

Binciken yan sanda ya sanya an kama mutane biyar da ake zargi da kisa da birne yan bangar ba bisa ka'ida ba.

An kama basarake kan kisan yan banga

Bayan kama mutanen da ake zargin, yan sanda sun cafke basaraken Utit Antai mai suna Okon Asuquo Etoekpo.

Kara karanta wannan

An harbe ƙasurgumin ɗan bindiga da ya sace manyan mutane a Najeriya

Jaridar Punch ta wallafa cewa ana zargin basaraken ne da ba wadanda aka tuhuma da kisan gillar kariya.

An harbe dan bindiga a Akwa Ibom

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Akwa Ibom ta sanar da cafke wani ƙasurgumin shugaban yan bindiga mai garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun harbe babban dan bindigar ne bayan sun yi musayar wuta a wani kazamin fada da suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng