Na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo
- Mutane hudu sun fada komar jami'an 'yan sandan jihar Neja bayan kamasu da kan mutum
- Shugaban ma su laifin, Abdullahi Dogo, ya ce wasu mutane biyu ne suka bashi kwangilar samo kan mutum
- Ya ce ya gayyato abokansa su taya shi bayan ganin cewar ba zai iya aikin shi kadai ba
'Yan sanda a jihar Neja sun kama wasu mutane hudu da kan mutum a kauyen Sabon Pegi da ke karamar hukumar Mashegu.
Binciken 'yan sanda ya gano cewa wani mutum mai suna Abdullahi Dogo shine jagoran sauran mutanen da aka kamasu tare.
Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Dogo ya bayyana cewa ma su sayen sassan jikin mutum ne su ka dauke shi kwangilar tono mu su sabuwar gawa.
DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria
A cewar Dogo, mai shekaru 30, mutanen sun bashi kwangilar miliyan N2m domin ya samu musu kan mutum.
An kama Dogo tare da sauran abokansa; Suleiman Abubakar mai shekaru 50, Babuga Mamman mai shekaru 42, da Abubakar Abdullahi Mai shekaru 31.
Dogo, wanda ya bayyana cewa shi makiyayi ne, ya ce wasu mutane biyu; Nasiru Koko, mazaunin jihar Kebbi, da Muhammadu mazaunin Sabon Pegi a karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.
DUBA WANNAN: Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu
"Sun sanar da ni cewa na je makabar kauyen Kanti na samo musu kan mutum bisa alkawarin Za su bani N2m.
"Daga ba zan iya aikin ni kadai ba, Sai na gayyato abokaina, na sanar da su kwangilar da aka bani, mun tsara yadda zamu yi aiki bayan sun amince.
"Sai dai, mun yi rashin sa'a, an sanar da jami'an 'yan sanda na ofishin Ibbi cewa an ganmu a cikin makabarta.
"Mun yi kacibus da jami'an 'yan sanda a yayin da mu ke barin makabartar da misalin karfe 5:30am na safiyar ranar uku ga watan Oktoba," a cewar Dogo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng