Janar Abdulsalam Abubakar Ya Kawo Shawarar Yadda Za a Gyara Aikin Soja a Najeriya

Janar Abdulsalam Abubakar Ya Kawo Shawarar Yadda Za a Gyara Aikin Soja a Najeriya

  • Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Abdulsalam Abubakar ya yi magana kan yadda lamura ke tafiya a gudan soja
  • Janar Abdulsalam Abubakar ya bukaci a cire dukkan wasu tsare tsaren da suke kawo koma baya ga mata wajen shiga aikin soja
  • Tsohon shugaban ya fadi irin rawar da mata sojoji suka taka a baya da yadda za su kawo cigaba idan aka ba su cikakkiyar dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya ya halarci wani taron sojojin Najeriya da aka shirya a birnin tarayya Abuja.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya yi kira na musamman kan ba mata damar shiga aikin soja ba tare da fuskantar wani kalubale ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Abdussalami
Janar Abdulsalam Abubakar ya ba sojoji shawara. Hoto: The Giant of Africa
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da ministan tsaro, Badaru Abubakar sun halarci taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gudummawar mata a aikin soja

Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce nasarar sojojin Najeriya tana da alaƙa ne da gudunmawar jami'ai maza da mata.

Punch ta wallafa cewa Abdulsalam Abubakar ya kara da cewa mata suna bayar da gudummawa a harkar shugabanci da sauran ayyukan soja.

Maganar ba mata yanci a gidan soja

Saboda gudunmawar mata a soja, Abdulsalam Abubakar ya ce ya zama dole a samar da tsarin da zai ba su damar shiga aikin cikin sauki.

Ya kuma kara da cewa akwai buƙatar bayan sun shiga aikin a ba su dukkan damar da za su ba da gudunmawa ba tare da nuna banbancin jinsi ba.

Ministan tsaro ya goyi bayan Janar Abdulsalam

Kara karanta wannan

Shugaban kwadago ya yi zafafan bayanai bayan fita daga wajen 'yan sanda

Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya ce ya zama wajibi a canza tsare tsare ta yadda kowa zai ba da gudunmawa a aikin soja a Najeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce yau da gobe ta nuna cewa samun mata sojoji na kara inganta aikin soja.

Tinubu ya gana da Janar Abdulsalam

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Abdulsalam Abubakar, ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Janar Abdulsalam Abubakar ya tattauna da shugaba Bola Tinubu ne a kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi kawo cigaba a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng