Tsoho mai ran karfe: Tshohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar ya cika shekara 75 a duniya
- Mukaddashin shugaban kasan Nijeriya Farfesa Yemi Osibanjo ya tayi tsohon shugaban kasan Nijeriya, ritaya Janar Abdulsalam Abubakar murnar cika shekara 75 da haihuwa.
- Mai magana da yawun mukaddashin shugaban kasa Osibanjo, Laolu Akande, ya bayyana haka ne a wani sanarwa inda ya ke cewa mukaddashin shugaban kasan yana tare da iyalai da abokanan arziki na Janar Abubakar don taya shi murna
Legit.ng ta samu labarin cewa mukaddashin shugaban kasan ya lura da cewa rayuwar Janar Abubakar Abdulsalam kasu kashi biyu inda shi fitaccen ma’aikacin soja ne sannan kuma da irin rawar da ya taka a tarihin siyasar kasa.
A sanarwa, ” Mukaddashin shugaban kasa Osibanjo ya tuna baya yadda a 1999 Janar Abubakar ya samu nasarar canza kundin mulki daga hannun sojoji zuwa mulkin farar hulla a Nijeriya, sannan kuma ya yabawa kokarin da yayi wajen samar da hakan wanda ya kawo karshen mulki kama karya na soja.
“A cikin ‘yan kwanakin nan, a cewar mukaddashin shugaban kasa, Janar Abubakar ya bada gudunmawa tare da sa baki wajen ganin an gudunar da canjin mulki daga hannun tsohon jam’iyyar PDP zuwa hannun jam’iyyar APC ba tare da tashin hankali ba a zaben 2015, wannan ya nuna cewa lallai shi mai kishin kasa ne, sabis don al’umma da kuma sadaukarwa ga Najeriya don a samu ci gaba a kasar.
A karshe kuma mukaddashin shugaban kasa ya ma tsohon shugaban kasan addu’a ma cewa “Allah (S.W.T) ya kara ma shi tsawon kwana da rai da lafiya”.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng