Kaduna: Ƴan Bindiga Akalla 8 Sun Baƙunci Lahira da Suka Yi Arangama da Sojoji

Kaduna: Ƴan Bindiga Akalla 8 Sun Baƙunci Lahira da Suka Yi Arangama da Sojoji

  • Gwarazan sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindigar daji takwas a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
  • Gwamnatin Kaduna ta ce sojojin sun sheƙe ƴan ta'addar ne a lokacin da suka fita sintiri a kewayen Kamfanin Doka da Gayam
  • Kwamshinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya ce gwamnan Kaduna ya yaba da wannan nasara da aka samu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga takwas a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta ce sojojin sun samu wannan nasara ne yayin da suka fita sintiri a yankin Kampanin Doka da ke karamar hukumar Birnin Gwari.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna, sun cafke mai ba su bayanai

Sojojin Najeriya.
Dakarun sojoji sun yi nasarar murkushe ƴan bindiga takwar a jihar Kaduna Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Facebook

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X a safiyar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aruwan ya ce sojojin na kan aikin sintiri suka ci karo da ƴan bindigar, kuma nan take suka hallaka mutum bakwai daga cikin miyagun a musayar wuta.

Dakarun Sojoji sun kwato makamai a Kaduna

Ya ce a yayin artabun, sojojin sun kwato bindigun AK-47 guda uku, AK-47 Magazine guda takwas da harsasai 120.

Sauran abubuwan da suka kwato sun hada da babura shida, wayoyin hannu guda uku, na'urorin rediyon Baofeng guda biyu, da kuma tufafi kala biyu.

"A lokacin da sojojin suka kammala aikin sintiri za su koma sansani sai suka sake cin karo da ‘yan bindiga a kusa da Gayam. Nan take suka kashe ɗaya sauran kuma suka tsere,"

Kara karanta wannan

Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200, SEMA ta ɗauki mataki

- Samuel Aruwan

Gwamnan Kaduna ya yabawa sojoji

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya jinjinawa jami'an tsaron bisa wannan nasara da suka samu.

A karshe gwamnatin Kaduna ta bukaci al'umma da su kai rahoton duk wanda suka gani ɗauke da raunukan harbin bindiga domin ɗaukar matakin da ya dace.

An kama ɗan sanda da wasu mutum 19

A wani rahoton kuma hukumar tattara bayanan sirri DIA za ta ci gaba da tsare ɗan sanda da wasu da ake zargi da taimakawa ƴan ta'adda a Najeriya.

Wata babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ce ta amince DIA ta ci gaba da tsare waɗanda ake zargi na tsawon kwanaki 30.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262