Tsadar Rayuwa: CBN Ya Fadawa 'Yan Najeriya Gaskiyar Halin da Za a Shiga

Tsadar Rayuwa: CBN Ya Fadawa 'Yan Najeriya Gaskiyar Halin da Za a Shiga

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da bahasi kan mummunan halin da za a shiga saboda tsadar rayuwa a Najeriya a nan gaba
  • Bahasin da Babban Bankin kasar ya fitar ya nuna cewa yan Najeriya da dama za su shiga matsalar karyewar tattalin arziki
  • Sai dai rahoton ya bayyana hanyoyin da yake tunanin yan Najeriya za su bi wajen samo mafita kan biyan bukatun yau da kullum

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da rahoto kan barazanar da take fuskantar yan Najeriya.

CBN ya nuna cewa cikin watanni masu zuwa yan Najeriya da dama za su shiga ƙarancin kudi wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yanke matsaya kan turawa da aka zarga da daga tutar kasar Rasha

Bankin CBN
Bankin CBN ya fitar da rahoto kan tsadar rayuwa. Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Talata ne bankin ya fitar da rahoton wajen yin bayani kan yadda tashin farashi ya gudana a watan Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar rashin kuɗi a Najeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi hasashen cewa nan da watanni masu zuwa al'umma da dama za su fuskanci ƙarancin kudi.

Binciken da bankin CBN ya yi ya nuna cewa kaso 83.7 na mutane sun koka kan tsadar rayuwa wanda hakan ke hasashen abubuwa za su kara tabarbarewa a gaba.

CBN: 'Za a dawo cin bashi sosai'

Rahoton da CBN ya fitar ya nuna cewa idan aka samu ƙarancin kudi, mafi yawan gidaje za su dawo cin bashi ne domin biyan bukatunsu.

Ya kuma kara da cewa wasu mutanen za su karar da kudin da suka tara ne wajen sayayyar kayan masarufi idan ba su ci bashi ba.

Kara karanta wannan

Sama da mutane miliyan 30 na cikin yunwa, gwamnati ta kawo hanyar wadatar da abinci

Bankin CBN ya ba gwamnati shawara

Rahoton ya nuna cewa akwai buƙatar gwamnati ta kara kirkiro dabarun tattalin arziki da za su bunkasa tattalin Najeriya.

Rahoton ya ce hakan ne zai kawo saukin lamura kan yadda ake hasashen karancin kudi daga yanzu har zuwa watan Nuwamba.

Kwace lasisin bankuna: CBN ya yi bayani

A wani rahoton, kun ji cewa Bankin CBN ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris, Wema da kuma Unity.

Muƙaddashiyar kakakin CBN, Hakama Sidi Ali, ta yi ƙarin haske kan takardar da ke yawo a wata sanarwa da ta fitar kan kwace lasisin bankunan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng