IMF Ya yi Magana kan Tsare Tsaren Tinubu, Ya Fadi Hanyar Kawo Saukin Rayuwa
- Asusun bada lamuni na duniya, IMF ya yi magana kan haɓakar tattalin arziki da aka samu a Najeriya a shekarar 2024
- Wakilin IMF a Najeriya ya bayyana cewa an samu haɓakar tattali ne bisa tsauraran matakan da gwamnati ta dauka
- Christian Ebeke ya fadi hanyoyin da za a bi wajen samun haɓakar tattalin arziki da kawo cigaba a harkar kasuwanci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Asusun bada lamuni na duniya ya yi magana bayan an samu haɓakar tattalin arziki a Najeriya zuwa 3.1%.
Wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke ne ya yi bayani yayin wani taron bunƙasa tattalin Najeriya da aka yi a jihar Legas.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Christian Ebeke ya ba Najeriya shawarar koyi da Indiya wajen harkar kasuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haɓakar tattalin arziki a a Najeriya
Wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke ya bayyana cewa an samu haɓakar tattalin arziki a Najeriya a 2024 da kaso 3.1%.
Tribune ta wallafa cewa asusun bada lamunin ya ce a shekarar 2023 matakin haɓakar tattalin arzikin Najeriya na kaso 2.9%.
Dalilin haɓakar tattalin Najeriya
IMF ya bayyana cewa an samu dalilin haɓakar tattalin ne saboda tsauraran matakan da gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta dauka.
Christian Ebeke ya ce idan Najeriya ta cigaba da daukan matakan da suka dace tattalin Najeriya na GDP zai haura zuwa 6.4% nan da shekaru uku.
Ana sa ran cewa idan aka samu habakar tattalin, al'umma za su samu saukin rayuwa da wadatar arziki.
Asusun IMF ya fadi matsalolin Najeriya
IMF ya bayyana cewa matsalolin da suka addabi Najeriya sun hada da talauci, yawan haraji, cin hanci da rashin rashin wutar lantarki.
Sai dai IMF ya bayyana akwai abin farin ciki idan aka fahimci cewa dukkan matsalolin za a iya magance su.
IMF ya bukaci a karasa cire tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi sabon kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafi a Najeriya.
IMF ya yi kiran ne kan bukatar kammala cire tallafin lantarki tare tabbatar da cewa hakan ne hanyar gina tattalin arziki a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng