Rashin Tsaro: An Kama Jigon PDP da Zargin Laifin Mallakar Makami

Rashin Tsaro: An Kama Jigon PDP da Zargin Laifin Mallakar Makami

  • Rundunar yan sanda ta sanar da cewa ta kama jigon jami'yyar PDP a jihar Bayelsa bisa zargin mallakar makami ba bisa ka'ida ba
  • Mataimakin sakataren yada labaran PDP, Amadein Tibieni ya shiga hannu ne bayan ya ƙubuta daga kamun da aka masa a baya
  • An ruwaito cewa Tibieni ya kasance daya daga cikin masu ta da kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a da

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bayelsa - Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama mataimakin sakataren yada labaran jami'yyar PDP a jihar Bayelsa.

Rahotanni na nuni da cewa rundunar yan sanda ta kama Amadein Tibieni ne bisa zargin mallakar makamai ba kan ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

Bayelsa
Yan sanda sun kama jigon PDP a Bayelsa. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kama Amadein ne bisa wani zargi da aka masa tun a shekarar 2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru da jigon PDP a 2021

A shekarar 2021 aka kama wani mutum mai suna Richard Okon bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Biyo bayan binciken yan sanda, Richard Okon ya bayyana cewa bindigar da aka kama shi da ita mallakar Amadein Tibieni ce.

An kama jigon PDP kan mallakar makami

Daily Trust ta wallafa cewa an kama Amadein Tibieni ne bisa zargin mallakar makamai wanda laifi ne a dokar kasa.

Rundunar yan sanda tana rike da Amadein Tibieni inda ake masa bincike a wajen binciken masu manyan laifuffuka.

An taba kama jigon PDP a baya

Rahotanni sun nuna cewa an taba kama Amadein Tibieni a baya amma saboda alaka da manyan mutane da yake da ita ya fita.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

Rundunar yan sanda ta yi zargin cewa a wannan karon ma yana kiran manyan mutane domin su ƙubutar da shi.

An kama mutum dauke da makamai a Jos

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani mutum dauke da makamai a cikin wata jaka da ya ke yawo da ita a garin Jos, jihar Plateau.

Wasu fusatattun matasa da suka fara damke mutumin, sun yi kokarin halaka shi bayan ganin makaman amma aka kira 'yan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng