Maganar Kudin Tallafin Man Fetur Ta Dawo Sabuwa, Gwamnati za Ta yi Bincike
- Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike domin gano hakikanin halin da ake ciki kan kudin tallafin man fetur na N2.7tn
- An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta nada mai binciken kudi na musamman da zai gano abin da ke faruwa a NNPCL
- Kamfanin NNPCL ya yi bayani kan kudin tallafi da yake bin gwamnatin tarayya duk da cewa an cire tallafin mai a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya za ta yi bincike kan kudin tallafin man fetur da kamfanin NNPCL ke binta.
Hakan na zuwa ne bayan kamfanin NNPCL ya bayyana cewa yana bin gwamnatin bashin N2.7tn na tallafin mai.
Jaridar Punch ta wallafa cewa za a dauko mai bincike ne na musamman domin gano sahihancin maganar kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL na bin gwamnati kudin tallafin mai
Tun hawan mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023 ya ce ya cire tallafin man fetur a Najeriya.
Amma duk da haka shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya bayyana cewa suna bin gwamnatin tarayya bashin kudin tallafi N2.7tn.
Za a yi bincike kan kudin tallafin mai
Biyo bayan haka aka samu sanarwa daga gwamnatin tarayya kan cewa za a yi bincike kan kudin tallafin.
Daily Post ta wallafa cewa an nada mai bincike na musamman da zai taimakawa ofishin mai binciken kudi na kasa kan gano halin da ake ciki.
Wane mai binciken kudi za a dauko?
A halin yanzu ba a ambaci wanda zai yi binciken kudin ba sai dai an samu bayanai kan cewa an fara ƙoƙarin zakulo shi.
Ministan kudi, Wale Edun ya bayyana cewa za a kammala binciken cikin gaggawa tare da yin fatan samun nasara.
Atiku ya caccaki Tinubu kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya.
Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda Bola Tinubu ya gaza yiwa ƴan kasa bayani kan lamarin tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng