Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Sokoto ba Ta Biya Kudin Fansar Sarkin Gobir ba

Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Sokoto ba Ta Biya Kudin Fansar Sarkin Gobir ba

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce bai gaji komai daga gwamnatin baya ba da zai yi amfani da shi wajen yaki da 'yan ta'adda ba
  • Ahmed Aliyu ya ce da ace gwamnatin Aminu Tambuwal ta kafa rundunar 'yan banga to da ya samu sauki wajen magance rashin tsaron
  • Game da batun kin biyan kudin fansa domin karbo sarkin Gobir da 'yan bindiga suka kashe, gwamnan ya ce yin hakan ya saba doka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu ya yi magana kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar Sokoto, musamman a 'yan kwanakin nan da ake ta garkuwa da mutane.

Mai girma Ahmad Aliyu ya ce tun a zamanin tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal aka samu wani gibi a yaki da 'yan bindiga, wanda ya ke kokarin cikewa.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Gwamnatin sokoto ta yi magana kan biyan kudin fansar sarkin Gobir
Gwamnan Sokoto ya bayyana dalilin gwamnati na kin biyan kudin fansar sarkin Gobir. Hoto: @honnaseerbazzah
Asali: Twitter

Gazawar Tambuwal a tsaron Sokoto

Hon. Nasir Bazza, babban mataimaki na musamman a kan kafafen sadarwa da soshiyal midiya ga Gwamna Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mai magana da yawun gwamnan:

"Dole ne a nanata cewa sojoji ba su samu nasara a yaki da 'yan bindiga a lokacin Tambuwal ba saboda ba su da karfin da za su iya kai hare-hare a lokaci guda a dukkanin kananan hukumomin jihar.

Da a ce gwamnatin Tambuwal ta kafa rundunar ‘yan banga, to da Gwamna Ahmed Aliyu ya samu abin da zai dora aiki a kansa. Sai dai, bai samu komai ba, dole ya fara daga tushe."

Batun kudin fansar sarkin Gobir

Mai magana da yawun gwamnan ya ce gwamnatocin duniya ba wai na Sokoto kadai ba, ba sa biyan kudin fansa ko yin sulhu da 'yan ta'adda, saboda zai bude kofar da za a gagara rufewa

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

"Da dace gwamnatin Sokoto ta biya kudin fansar hakimin da aka sace, da zuwa karshen shekara ta biya biliyoyi duk da sunan karbo mutane daga hannun 'yan bindiga.
"Na farko dai hakan zai sa 'yan bindigar sun yi amfani da kudin wajen kara sayo makamai, kuma ba lallai ne su sako wanda suka tsaren bayan karbar kudin ba."

Dokar hana biyan kudin fansa

Hon. Nasir Bazza ya ci gaba da cewa, da ace gwamnatin jihar ta biya kudin fansar karbo basaraken, to da ta sabawa dokar yaki da ta'addanci ta Najeriya ta 2023.

"Dokar ta haramtawa jihohi, iyalai ko abokan wadanda aka yi garkuwa da su biyan 'yan bindiga kudin fansa. Dokar ta na kokarin magance matsalar sace mutane da neman kudin fansa."

- A cewar mai magana da yawun gwamnan.

Sokoto: An kashe sarkin Gobir

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindigar da suka sace sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Isa Bawa sun harbe shi har lahira yayin da suka ci gaba tsare dansa.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun kashe basaraken ne bayan wa'adin da suka diba na kai kudin fansarsa ya kare, kwanaki bayan fitar da bidiyonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.