Sojoji Sun Bayyana Dalilin Janyewa daga Yankunan da Ke Fama da 'Yan Bindiga

Sojoji Sun Bayyana Dalilin Janyewa daga Yankunan da Ke Fama da 'Yan Bindiga

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi bayani kan dalilin da ya sanya dakarun sojoji suka janye daga wasu ƙauyukan jihar Neja
  • Kakakin DHQ ya bayyana cewa an janye sojojin ne biyo bayan hare-haren da ƴan bindiga ke kai musu saboda rashin kyawun hanyoyin wajen
  • Ya bayyana cewa za a mayar da sojojin da zarar an kammala samar da dabarun da za su ba su damar yin galaba kan ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana dalilin da ya sanya dakarun sojoji suka janye daga yankunan da ke fama da matsalar ƴan bindiga a jihar Neja.

DHQ ta bayyana cewa sojojin sun janye ne saboda dalilai na sauya salon yadda suke tunkarar ƴan bindiga a yankunan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun hallaka jami'in tsaro, ,sun sace manoma

Sojoji sun janye daga kauyukan jihar Neja
Sojoji sun yi bayanin dalilin janyewa daga kauyukan jihar Neja Hoto: Headquarters Nigerian Army
Asali: Facebook

Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka janye sojojin?

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an janye sojojin ne a watan Afirilu biyo bayan mummunan kwanton ɓaunan da ƴan bindiga suka yi musu.

Ya yi bayanin cewa sojojin sun yi asarar rayuka da kayan aiki bayan sun taka bama-baman da ƴan bindiga suka dasa musu.

Yaushe sojojin za su koma?

Yayin da yake bayyana janyewar sojojin a matsayin na wucin gadi, ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba sojojin za su koma yankunan bayan kammala nazari kan dabarun yadda za a ɓullowa ƴan bindigan.

A cewar kakakin, ƴan bindigan suna amfani da rashin kyawun hanyoyin yankin domin kai farmaki ga sojoji.

"A wani lokaci cikin watan Afirilun 2024, an janye dakarun sojoji na sansanin FOB da ke Alawa a jihar Neja na wucin gadi zuwa wani sansanin FOB da ke kusa."

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin lulawa ƙasar waje, COAS ya yi magana mai zafi kan masu kiran juyin mulki

"Za a mayar da su bayan an kammala yin gyare-gyare ta yadda za su samu damar samar da tsaro a yankin."

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na runduna ta ɗaya a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka wani ɗan ta'adda yayin musayar wuta.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a hannun ƴan ta'addan a wani samame da suka kai a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng