Salon Yaki Ya Canza: Gwamna Ya ba da Izinin Luguden Wuta ga Yan Bindiga

Salon Yaki Ya Canza: Gwamna Ya ba da Izinin Luguden Wuta ga Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina tayi zaman masu ruwa da tsaki kan abin da ya shafi matsalar yan bindiga da ta ki ci ta ki cinyewa
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya tara jami'an tsaro, sarakuna da sauran al'umma daga kananan hukumomi 19 na jihar Katsina
  • Gwamnatin ta fitar da umarnin kai zafafan hare hare babu ƙaƙƙautawa kan yan bindiga a dazuka domin samar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabon tsari kan yaki da yan bindiga da suka addabi mutane.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya sanar da tsarin ne bayan ya jagoranci zama da masu ruwa da tsaki a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Garkuwa da Mutane: Likitoci sun tafi yajin aiki saboda garkuwa da wata likita tun 2023

Gwamna Dikko Radda
Za a yi luguden wuta ga yan bindiga a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan abin da ya faru a taron ne cikin wani sako da jami'in yada labaran gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Izinin luguden wuta ga yan bindiga

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da yin luguden wuta ga yan bindiga a ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro.

Dukkan jami'an tsaro ne za su yi haɗaka domin kai zafafan hare hare maboyar yan ta'adda na tsawon kwanaki 30 domin kakkaɓe su.

Gwamna ya ba sarakuna umarni kan tsaro

Daga cikin abubuwan da gwamnatin Katsina ta fitar bayan taron akwai kira na musamman ga sarakunan gargajiya.

Gwamnatin ta buƙaci hadin kan sarakuna wajen yin addu'a, neman hadin kai yayin fada da yan bindiga da samar da tsaro.

Hadin kan mutane wajen yakar yan bindiga

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Gwamnatin Katsina ta yi kira ga al'ummar jihar kan ba jami'an tsaro hadin kai wajen gudanar da aikin.

Haka zalika gwamna Radda ya umarci jama'a da su ba jami'an tsaro bayanan sirri da za su taimaka wajen gano makircin yan ta'adda.

Sarkin Katsina ya yi babban rashi

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya rasa Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hassan Kabir Usman.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tura sakon ta'aziyya ga mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng