Fada Ya Barke Tsakanin Makiyaya da Manoma a Arewacin Najeriya, an Kashe Mutum

Fada Ya Barke Tsakanin Makiyaya da Manoma a Arewacin Najeriya, an Kashe Mutum

  • Ana fargabar makiyaya sun kashe wani manomin Gbagyi a kauyen Barkta da ke cikin karamar hukumar Bosso ta jihar Neja
  • An ruwaito cewa makiyayan sun kashe manomin ne lokacin da ya tunkare su kan barin shanunsu suka yi barna a gonarsa
  • Mazauna kauyen Gbagyi sun dauki zafi kan kisan dan garinsu inda su ma suka kai harin ramuwar gayya a kauyen Barka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wani rikici ya barke tsakanin mutanen kauyen Gbagyi da makiyaya a kauyen Barkta da ke cikin karamar hukumar Bosso ta jihar Neja.

An ce rikicin ya faro ne tun a ranar 26 ga watan Agustan 2024, bayan hatsaniya da ta barke tsakanin wani manomi da wasu gungun makiyaya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar rikicin yan Shi'a da yan sanda, tarzoma ta ƙara tashi a Abuja

Fada ya kaure tsakanin makiyaya da manoma a jihar Neja
Neja: Ana fargabar an kashe mutum daya yayin da fada ya kaure tsakanin makiyaya da manoma
Asali: Original

Makiyaya sun kashe manomi

Fitaccen mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta shaida wa Makama cewa an fara fadan ne lokacin da manomin ya tunkari makiyayan kan shigar da shanunsu cikin gonarsa, lamarin da ya yi sanadin lalata shukoki.

A yayin wannan takkadama, an yi zargin cewa makiyayan sun kashe manomin, wanda hakan ya haifar da tarzoma a kauyen Gbagyi.

Manoma sun yi ramuwar gayya

A matsayin ramuwar gayya kan mutuwar manomin, mutanen kauyen Gbagyi sun kai hari a matsugunin makiyayan da ke kusa da kauyen Barkta, a cewar rahoton.

An ce hakan ya haifar da kazamin fada tsakanin kungiyoyin biyu, lamarin da ya jawo tashin hankali a gaba daya yankin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

A halin yanzu dai kura ta lafa a kauyen Barkta, amma har yanzu mazauna yankin na cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

Rahoton ya ce majiyoyi daga yankunan sun sun bayyana damuwa game da yiwuwar ƙarin tashin hankali ko ɗaukar fansa daga bangarorin.

An kashe mutane a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa rikicin makiyaya da manoma da ya barke a yankin gandun dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa, jihar Jigawa ya jawo asarar rayuka.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu ya tabbatar da lamarin inda ya ce akalla mutane uku ne ake fargabar an kashe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.