Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnoni 6 Sun Bindige N160bn a Gina Filayen Jiragen Sama

Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnoni 6 Sun Bindige N160bn a Gina Filayen Jiragen Sama

  • 'Yan siyasan adawa da kwararu a harkar sufurin jiragen sama sun nemi a binciki wasu gwamnonin jihohohin Najeriya shida
  • Ana zargin gwamnatocin Ekiti, Ebonyi, Jigawa, Yobe, Nasarawa, da Bayelsa sun kashe N160bn wajen gina filayen jiragen sama
  • A yayin da aka nemi jama'a su tuhumi gwamnonin kan almubazzaranci, an kuma bukaci mayar da filayen zuwa cibiyar ba da horo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ana zargin gwamnatocin jihohi shida da suka hada da Ekiti, Ebonyi, Jigawa, Yobe, Nasarawa, da Bayelsa sun kashe kimanin N160bn a kan gina filin jirgin sama.

'Yan siyasan adawa da kwararu a harkar sufurin jiragen sama sun bayyana hakan a matsayin almubazzaranci da kudi kan abin da ba zai yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

Masana da 'yan adawa sun yi magana kan gina filayen jiragen sama a wasu jihohi 6
An caccaki wasu gwamnoni 6 kan kashe N160bn wajen gina filayen saukar jiragen sama. Hoto: Santiago Urquijo
Asali: Getty Images

An soki gwamnoni kan kashe N160bn

Jaridar The Punch ta ruwaito masu ruwa da tsakin sun ce makudan kudaden jama'a da gwamnonin suka kashe a ayyukan sun tashi a asara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi Allah-wadai da gwamnonin jihohin tare da rokon ’yan Najeriya da su dora musu alhakin barnatar da dukiyarsu.

Duk da haka, wasu masu ruwa da tsakin sun ba da shawarar cewa a mayar da filayen jiragen zuwa cibiyoyin koyon kasuwanci domin amfanin al'umma.

Wasu sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki kudaden da aka kashe wajen ayyukan da ba su dace ba.

Gwamnoni sun tsiri gina filayen jirgi

Wani bincike ya nuna cewa jihohin shida sun kashe kimanin N160bn wajen gina filayen jirgin sama daban-daban, amma babu wasu jiragen a zo a gani da ke amfani da filayen.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Duk da kalubalen da manyan jiragen sama na kasa ke fuskanta na rashin ciniki, gwamnatocin jihohi da dama sun ci gaba da kashe makudan kudade a gina karin filayen jiragen.

A cikin shekaru goma da suka gabata, gwamnatocin jahohi a kusan 10 ne suka fara aiwatar da irin wadannan ayyuka na gina filin jiragen sama duk da an gargade su kan rashin alfanunsa.

Wasu daga cikin jihohin sun hada da Osun, Ebonyi, Ogun, Benue, Zamfara, Nasarawa, Abia, Ekiti, da Bayelsa.

Masana sun yi magana

Babban sakatare na kungiyar tsaron sufurin jiragen, Olumide Ohunayo, ya soki yadda wasu gwamnoni ke tattago aikin gina filayen jiragen sama.

Ya yi jayayya cewa yayin da gina filayen jiragen sama ke da muhimmanci, ya ce sau da dama kudaden da ake kashewa wajen aikin na wuce kima, kuma karshe a karkatar da su

Gwamnan Zamfara na shan suka

A wani labarin, mun ruwaito cewa al'umma sun yi wa gwamnan Zamfara ca kan aikin gina filin saukar jiragen sama da ya tattago duk da cewa jihar na fama da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki Tawagar wani kwamishina a Oyo, an ga hotunan barnar

An ce Gwamna Dauda Lawal ya dauki aniyar kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina katafaren filin jirgin sama a babban birnin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.