"An Sha Wahala": Rundunar Sojoji Ta Faɗi Matsayarta kan Kiran Kifar da Gwamnatin Tinubu
- Rundunar sojojin Najeriya ta sake nanata matsayarta kan kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Bola Tinubu
- Hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya ce su na sane da yadda wasu ke neman a kifar da gwamnati
- Amma a cewar Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ba za su rusa ƙimar da su ka sha wahala shekaru 25 su na ginawa ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Akwa Ibom - Babban hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya ce ba za su saurari masu son juyin mulki ba.
Manjo Janar T. A Lagbaja ya can babu yadda za a yi sojojin su wargaza ƙimarsu da su ka shafe shekaru 25 su na ginawa.
Sojoji sun magantu kan kiran juyin mulki
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban sojojin ya bayyana haka ne a wani taron babban hafsan sojoji da ya gudana a Uyo, jihar Akwa Ibom.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lagbaja ya yi tir da kiran da wasu 'yan kasar nan su ke yi daga ranar 1- 10 Agusta, 2024 kan tsadar rayuwa da adawa da manufofin Bola Tinubu.
Rundunar soji ta goyi bayan dimokuradiyya
Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojojin kasar na ta jaddada goyon bayanta ga haɓaka dimokuradiyya da kare martabarta duk da zugar wasu daga sassan Najeriya.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa babban hafsan sojojin, Taoreed Lagbaja ne ya bayyana haka, inda ya ce kiran bai dace ba.
Manjo Janar Lagbaja ya ce mutanen da ke neman sojoji su tunɓuke zaɓaɓɓiyar gwamnati ba su san komai ba, kuma ba su da labarin gwagwarmayar da aka yi.
Tinubu ya yi martani kan juyin mulki
A baya mun ruwaito cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya shawarci matasan kasar nan da ka da su bari wasu tsiraru su yi amfani da su wajen tayar da fitina.
A jawabinsa ga matasa yayin zanga-zangar adawa da.manufofinsa, Tinubu ya bayyana cewa a haɗa hannu wajen cigaban ƙasa ba rarrabuwar kawuna ba.
Asali: Legit.ng